Back

Majalisar Wakilai za ta binciki tserewar da jami’in Binance ya yi daga gidan kaso

Majalisar Wakilai ta ƙuduri aniyar gudanar da bincike kan lamarin da ya kai ga tserewar Mista Nadeem Anjarwalla, jami’in wani kamfani na musayar kuɗin crypto, Binance.

Hakan ya biyo bayan amincewa da ƙudirin da ɗan majalisa Dominic Okafor (LP-Anambra) ya gabatar a zaman majalisar da aka yi ranar Laraba a Abuja.

Idan dai ba a manta ba Gwamnatin Tarayya ta kama Anjarwalla tare da tsare shi a ranar 26 ga watan Fabrairu, bisa zarginsa da haɗa baki da kamfanin wajen halasta kuɗaɗen haram da kuma bada tallafin ta’addanci.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya rawaito cewa jami’an biyu na Binance an buƙaci su bayyana a gaban kotu a ranar 4 ga watan Afrilu, domin amsa laifukan da ake zargin su yi wa Nijeriya kafin matsalar tsaron.

Ɗan majalisar ya ce tserewar da babban jami’in Binance ya yi daga ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro ta hanyar amfani da “fasfo ɗin da aka yi fasa-ƙwaurinsa” ya kasance abin takaici, abin kunya, da abin damuwa.

Ya ce hakan ya nuna wa duniya irin tsarin tsaron da ƙasar ke da shi wanda baida ishashshen kariya.

Majalisar ta kuma umarci Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da ya ɗauki nauyin gudanar da bincike tare da gurfanar da jami’an da aka samu da hannu wajen tserewar Anjarwalla.

Majalisar ta kuma umarci kwamitoci kan laifukan kuɗi, Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro, leƙen asiri, da na cikin gida da su tabbatar da bin umarnin tare da gabatar da rahoto ga majalisar nan da makonni biyu.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?