Majalisar zartaswa ta tarayya (FEC) ta amince da cikakken aiwatar da rahoton Stephen Oronsaye na hada wasu hukumomin gwamnati da wasu, yayin da wasu kuma za a soke su.
An yanke wannan shawarar ne a taron majalisar zartaswar da shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a ranar Litinin.
Wannan a cewar mai baiwa shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin siyasa Hadiza Bala Usman, ya yi daidai da bukatar rage tsadar harkokin mulki da kuma daidaita yadda ake tafiyar da harkokin gwamnati.
Domin tabbatar da aiwatar da sauye-sauyen da ake shirin yi, majalisar ta kafa wani kwamiti da ke da hurumin aiwatar da hadakar, da soke-soke, da sake tsugunar da su a cikin makonni goma sha biyu.
Har ila yau majalisar ta kuma samu rahoto daga kwamitin ma’aikatun da aka kafa domin duba al’amuran shirin zuba jari na kasa.
Majalisar ta kuma amince da sake fara biyan kudi kai tsaye ga gidaje miliyan goma sha biyu da suka kunshi ‘yan Najeriya miliyan sittin tare da wasu muhimman tsare-tsare.
A shekarar ta dubu biyu da sha daya ne, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kafa kwamitin shugaban kasa kan sake fasalin tsarin mulki da kwamitoci da hukumomin gwamnatin tarayya inda Oronsaye ya zama shugaba.
A ranar sha shida ga watan hudu na shekara ta dubu biyu kwamitin ya gabatar da wani rahoto mai shafuka dari takwas wanda ya gano, a tsakanin wasu abubuwa da dama, hukumomin da suka yi karo da juna, suna haddasa almubazzaranci a cikin kashe kudi.
Rahoton ya ce akwai ma’aikatu, kwamitoci da hukumomi 541 inda ya bayar da shawarar cewa a rage 263 daga cikin hukumomin zuwa 161, a soke hukumomi 38 sannan a hade guda 52.
Akwai wasu kudurori ba tare da an motsa su ba a kan rahoton a lokacin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari na tsawon shekaru takwas amma sabuwar gwamnatin Tinubu ta ce aiwatar da rahoton ya yi daidai da matakan rage kashe kudade.