Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON), ta bayyana cewa, ya zuwa ƙarshen rijistar maniyyata, 51,447 ne kawai suka yi rijistar zuwa aikin hajjin 2024 daga Nijeriya.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktar Hulɗa da Jama’a ta NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta fitar.
A cewar sanarwar, gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta taka rawar gani wajen ganin an cimma wannan kyakkyawar manufa. Ta kuma yaba da gudunmawar da gwamnatocin jihohi da sauran masu ruwa da tsaki suka bayar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Hukumar Alhazai ta Ƙasa, (NAHCON), ta amince da ɗimbin sadaukarwar da Gwamnatin Tarayya ta yi a kan duk wata matsala da ta ke fuskanta wajen ganin an samu sauƙin matsalolin da ke addabar maniyyata.
“Hukumar ta kuma yaba da haƙurin da maniyyata suka nuna a cikin rashin tabbas. Hukumar ta lura da damuwar da Malamai suka nuna kan halin da maniyyata ke ciki. Masu ruwa da tsaki da dama, ciki har da Gwamnonin Jihohi, sun ba da mafita daga ƙangin. Wasu kafafen yaɗa labarai sun nuna matuƙar fahimtar matsalolin da a zahiri suka fallasa gaskiyar lamarin da Hajjin 2024 ke fuskanta.
“Haƙiƙa, shirye-shiryen Hajjin 2024 ya zo da ƙalubalen da ba a zata ba wanda aka koyo darussa. Hukumar ta NAHCON ta sani cewa, tsare-tsare na dogon lokaci shi ne dabarun da za a iya aiwatar da su da za su shawo kan ƙalubalen da suka kawo tsaiko a shirye-shiryen Hajjin bana.
“A nan gaba, tsare-tsare na dogon lokaci shi ne tsarin da Hukumar za ta bi wajen gudanar da ayyukanta kafin aikin Hajji. Gaskiya ne cewa duk masu ruwa da tsaki a aikin Hajji dole ne su bi sahu domin kaucewa ƙalubalen da ba a zata ba.”