Back

Marwa ya yabawa gwamnatin Burtaniya kan Samar da hedikwatar jami’an EFCC a bakin tekun Eko Atlantic 

Shugaban Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagu Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), Birgediya Janar Mohammed Buba Marwa (Mai Ritaya), ya yabawa gwamnatin Burtaniya bisa tayin ɗaukar nauyin samar da hedikwata da masaukin jami’an sashin ruwa na yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi a bakin tekun Eko Atlantic.

Marwa, wanda ya yi wannan yabo a lokacin da yake ƙaddamar da fara aikin da Hukumar Ayyuka ta Ƙasa da Ƙasa na Ofishin Gida na Burtaniya (HOIO) ta gudanar, ya bada tabbacin cewa hukumar za ta ci gaba da aiwatar da abin da ‘yan Najeriya da abokan hulɗar ta na ƙasa da ƙasa suke tsammani.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Bayar da Shawarwari na hedikwatar NDLEA, Abuja, Femi Babafemi, ya fitar a ranar Laraba, ashirin da takwas ga watan Fabrairu.

Ya ce amincewa da hukumar da Shugaba Bola Tinubu da gwamnatin Birtaniya suka yi da kuma goyon bayansu na kowane lokaci zai zama abin ƙara ƙarfafa gwiwa ga jami’ai da maza masu yin kasada sosai wajen wargaza ƙungiyoyin miyagun ƙwayoyi a kullum.

Marwa ya ce, manufar kawai ita ce a daƙile illolin shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da safarar miyagun ƙwayoyi a Najeriya, tare da bayar da gudummawa sosai ga ƙoƙarin da duniya ke yi na magance matsalar miyagun ƙwayoyi.

Ya yi nuni da cewa, ofishin da wuraren kwana da gwamnatin Birtaniya ke yi wa ma’aikatan sashen ruwa na hukumar zai ƙara musu lafiya da inganci da kuma ƙwarin gwiwa ba sosai.

“Kun ba mu wuri a nan, kun ba mu horo, kun tallafa mana da jiragen ruwa da gyarawa da kuma wurin kwana. Sai dai mu ce mun gode. Muna so mu ba da tabbacin abin da kuka riga kuka sani cewa NDLEA babbar hukuma ce, muna yin abin da ya kamata mu yi ba tare da tsoro ko alfarma ba, za mu yi aikin, zan iya ba ku tabbacin hakan yayin da muke ci gaba da haɗin gwiwa. Mun gode sosai”, in ji shugaban hukumar ta NDLEA a lokacin da yake jawabi ga jami’an gwamnatin Burtaniya da ‘yan kwangilar su a wurin da ake gudanar da aikin.

Ya kuma yabawa jami’an sojin ruwa, kwastam, shige-da-fice da sauran jami’an yankin bisa haɗin gwiwar da suke yi da NDLEA.

“Dole ne mu tashi tsaye tare, duk da cewa hukumar ta NDLEA ce kan gaba a wannan sana’ar, aikin na haɗin gwiwa ne. Dole ne mu haɗa gwiwa don yin aikin. An sanar da ni cewa akwai haɗin gwiwa da yawa da ke gudana kamar yadda na kasance a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Murtala Muhammed (MMIA) a safiyar yau kuma na yi magana da manyan abokan aikin ku a can kuma suna aiki tare kamar yadda kuke a nan. Ina roƙon ku da ku ci gaba da kasancewa a hakan kuma ina yi muku fatan samun nasara,” inji shi.

Da yake jawabi ga jami’an sashin, Marwa ya ce shugabancin hukumar na sake fasalin sashin na ruwa domin ya zama “mafi ƙarfi a ƙarƙashin ƙwararren kwamanda.”

Ya buƙace su da su “dage, ku tashi da ƙafafunku kuma ku yi aiki tuƙuru don ganin cewa ƙwayoyi ba su wuce ta ruwa ba.”

Wakilin Ofishin Harkokin Cikin Gida na Burtaniya, Kris Hawksfield, ya ba da tabbacin cewa za a kammala aikin nan da Yulin 2024.

Da yake jawabi tun da farko a wajen wani taron goyon baya ga yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi (WADA) da shugabannin Ƙungiyar Mawaƙa ta Najeriya (PMAN), Marwa ya ce akwai buƙatar ƙungiyar ta haɗa kai da hukumar wajen yaƙi da shan miyagun ƙwayoyi da fataucin miyagun ƙwayoyi.

Ya buƙaci shugaban PMAN, Prettywise Okafor da sauran shuwagabanni da su ja hankalin mambobinsu su yi amfani da basirar da Allah ya ba su domin amfanin al’umma maimakon amfani da waƙoƙinsu wajen tallata shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, musamman a tsakanin matasa.

A nasa martanin Okafor ya bayyana shirin PMAN na yin haɗin gwiwa da Hukumar. Ya kuma yi ƙarin bayani game da ƙoƙarinsu na shirya gangamin yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a faɗin ƙasar nan da kuma shirinsu na gina cibiyoyin gyara hali a wani ɓangare na ayyukan da suke gudanarwa a Abuja da Legas.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?