Wata tirela ɗauke da mangoro ta faɗa cikin wani masallaci da ke gidan Barade, daura da tsohon ofishin bayar da lasisi a garin Kontagora a Jihar Neja da sanyin safiyar Juma’a.
Majiyoyi sun shaida cewa masallata sun watse kenan bayan sallar Tahajud lokacin da lamarin ya faru.
An ce ɓangaren da abin ya shafa na masallacin inda mata da ƙananan yara suke yin sallar Tahajjud ne.
An bayyana cewa direban motar ya taso ne daga garin Bida na Jihar Neja, kuma yana kan hanyarsa ta zuwa Sokoto ne da fasinjoji huɗu a lokacin da barci ya ɗauke shi ya kauce hanya.
Tirelar ta tura ɗaya daga cikin motocin da aka ajiye a wajen Masallacin zuwa barandar Masallacin.
Wani mazaunin garin Yahaya Suleiman ya shaida cewa lamarin ya faru ne ƙasa da mintuna shida da tafiyar masallatan.
“Mun gode wa Allah. Gefen da motar ta faɗa ciki ɓangaren mata da yara ne na Masallacin. Jama’a sun gama sallar Tahajjud sun tafi lokacin da lamarin ya faru. Ba a rasa rai ba amma an yi ɓarna a Masallacin,” inji shi.
Ɗaya daga cikin fasinjojin da ke bayan motar mai suna Mustapha Sokoto, ya shaida cewa yana barci amma da ya farka ya samu kansa a ƙasa.
“Lokacin da abin ya faru, barci nake yi. Na tsinci kaina a kwance a ƙasa. Hakan ya faru da misalin ƙarfe 4 na safe.”
“Mun tashi daga Bida, mun nufi Sakkwato. Mu biyar ne a cikin motar; babu wanda ya samu rauni. Masu kayan suna cikin motar tare da direban. Ban san abin da ya faru ba saboda ina barci a bayan motar. Ina saman kayan da ke baya,” inji shi.