Masallata da dama sun mutu a wani masallaci da ya rufta lokacin sallar la’asar a Jihar Legas, ranar Lahadi.
Masallacin da ya rufta yana kan titin Yusuf, Papa Ajao, Mushin.
Blueprint ta gano cewa an gano mutane da dama daga cikin baraguzan ginin, waɗanda suka mutu da kuma waɗanda suka samu rauni, yayin da ake fargabar wasu da dama sun maƙale.
Da aka tuntuɓi Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Legas (LASEMA), Nosa Okunbor, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ana ci gaba da aikin ceto.
“Mutanenmu suna wurin yayin da nake magana da ku. Aikin ceto na ci gaba da gudana. Abin da zan iya faɗa kenan yanzu,” inji shi a wayar.