Back

Masarautar Saudiyya ta kashe dala miliyan 47.1 kan taimakon agaji a Nijeriya, inji Jakadan Saudiyya

Tan 50 na dabino da Masarautar Saudiyya ta ba Nijeriya

Jakadan Masarautar Saudiyya a Nijeriya, Faisal Ebraheem Alghamdi, ya bayyana cewa Saudiyya ta gudanar da ayyuka 98 a Nijeriya da kuɗinsu ya kai dala miliyan 47,194,210 a fannonin samar da abinci, kiwon lafiya, tsaftar muhalli da ilimin tsafta da kuma taimakon agaji.

Alghamdi wanda ya bayyana haka a yayin miƙa tan 50 na dabino ga Ma’aikatar Harkokin Wajen Ƙasar a ranar Juma’a, ya ce hakan na nuni da irin jajircewar da masarautar ta yi wajen samar da agaji ga al’ummar Nijeriya.

“A tsawon shekarun da suka gabata, Gwamnatin Saudiyya ta hannun Cibiyar Ba Da Agajin Jin Ƙai ta Sarki Salman (KSRelief), tana ba da taimakon jin ƙai ga Tarayyar Nijeriya a fannoni daban-daban; na baya-bayan nan shi ne aiwatar da Shirin Et’am 3 a watan Maris 2024 ta hanyar raba kwandunan abinci ga mutane 5606 da suka ci gajiyar tallafin a Kano, Jigawa, Katsina, Borno da Abuja, kan kuɗi dala 400,000.”

Yayin da yake bayyana Nijeriya a matsayin ƙasa mai sada zumunci da ‘yan uwantaka, ya ce ƙasashen biyu na da alaƙa mai ƙarfi ta al’adu da addini wanda nan ba da jimawa ba za ta bunƙasa zuwa kasuwanci.

Ya ci gaba da bayyana cewa dabinon na daga cikin tallafin jin ƙai da agajin da Mai Kula Da Masallatai Biyu Masu Alfarma ke gabatarwa a kowace shekara ga wasu ƙasashen sada zumunta da suka haɗa da Nijeriya.

“Bugu da ƙari kuma, Masarautar Saudiyya ta hannun Cibiyar Ba Da Agajin Jin Ƙai ta Sarki Salman (KSRelief) ta gudanar da wani aiki na tantance rashin lafiya a Abuja, Kano da Legas a cikin kwata na ƙarshe na 2023, inda aka ba da magani daban-daban kyauta ga ‘yan Nijeriya.

“Wannan da ma fiye da haka suna nuna alƙawurran da masarautar Saudiyya ta ɗauka na ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin ƙasashenmu biyu a kowane mataki, kuma Masarautar ta ƙuduri aniyar ci gaba da bayar da duk wani taimako ga Nijeriya.

A nasa ɓangaren, Mataimakin Darakta, Sashen Gabas ta Tsakiya da Yankin Gulf, na Ma’aikatar Harkokin Wajen Ƙasar, Jakada Murtala Jimoh, ya bayyana cewa alaƙar Nijeriya da Saudiyya za ta wuce aikin hajji ta haɗa da kasuwanci da tattalin arziƙi.

A halin da ake ciki, Ma’aikatar Harkokin Wajen Ƙasar ta miƙa tallafin tan 50 na dabino da masarautar Saudiyya ta bayar ga Ma’aikatar Kula da Ayyukan Jin Ƙai da Yaƙi da Fatara, domin rabawa ‘yan gudun hijira da waɗanda bala’o’i ya shafa a faɗin ƙasar.

Da yake jawabi a wajen gabatar da ‘ya’yan itatuwan a hukumance, Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Wajen Ƙasar, Jakada Adamu Lamuwa, ya bayyana ƙwarin gwiwa ga Ma’aikatar Jin Ƙai, wadda yake ganin ta fi kowa sanin yadda za a raba wa mabuƙata.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?