Back

Masu aika saƙonni marasa lasisi suna safarar makamai da miyagun ƙwayoyi, inji Hukumar Aika Saƙonni

Hukumar Aika Saƙonni ta Nijeriya (NIPOST) ta daƙile masu aika saƙonni marasa lasisi a Kaduna.

NIPOST ta rufe yawancin ofisoshi na masu aika saƙonni yayin wani aiki wanda Babban Manajan Sashen Kula da Aika Saƙonni (CLRD), Mista Shonde Dotun ya jagoranta.

Da yake jawabi bayan aikin, Dotun ya ce ayyukan masu aika saƙonnin marasa lasisi na ƙara matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta a halin yanzu.

Ya ce wasu daga cikinsu ‘yan ta’adda ne ke amfani da su wajen isar da bindigogi da muggan ƙwayoyi wanda hakan ke kawo cikas ga tsaron ‘yan ƙasa.

Dotun ya ce, “Muna nan Kaduna ne domin tsaftace kasuwar aika saƙonni da ta haɗa da masu aika saƙonni masu zaman kansu.

“Bincike ya nuna cewa muna da mutane da yawa da ke aiki ba tare da samun lasisi daga Babban Jami’in Harkokin Aika Saƙonni na Tarayya ba kamar yadda dokar NIPOST ta tanada.

“Akwai ƙa’idojin doka, amma akwai masu aika saƙonni masu zaman kansu da yawa ba tare da lasisin aiki ba.

“Don haka mun zo nan ne don tsabtace kasuwar don duba ayyukan masu aikata laifuka da samar da yanayi mai kyau ga waɗanda aka ba lasisin su ci gaba.”

Dotun ya ci gaba da cewa yawancin ma’aikatan da ba su da lasisin an same su da aikata haramun.

“Wasu daga cikin su sun tsunduma cikin samun kuɗi ta hanyar ƙarya. Wasu ba su da ofisoshi, wasu kuma suna yaudarar mutane.

“Wasu daga cikinsu ana amfani da su wajen ɗaukar ƙananan makamai da ƙwayoyi. Mun ga wasu daga cikinsu ɗauke da daloli. Suna amfani da su wajen watsa miyagun ƙwayoyi.

“Mun kama wasu daga cikinsu da hodar iblis a cikin biredi,” inji shi.

Ya ce tawagar tabbatar da doka ta NIPOST za ta faɗaɗa ayyukanta zuwa tashoshin motoci.

“Muna aiki kafaɗa da kafaɗa da ‘yan sanda don ganin an gurfanar da waɗanda aka kama,” inji shi.

Dotun ya bayyana cewa, a shekarar da ta gabata, an kama masu safarar miyagun ƙwayoyi 500 tare da gurfanar da su gaban kuliya, inda ya ƙara da cewa kawo yanzu sama da mutane 100 ne aka kama a aikin da aka fara a Kano.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su daina amfani da masu aika saƙonni da ba su da lasisi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?