Back

Masu gurasa sun yi zanga-zanga kan tsadar fulawa a Kano

‘Kungiyar masu sana’ar burodi (Gurasa) a Kano, ta yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da masu ruwa da tsaki da su gaggauta daukar matakai domin tallafawa talakawa ta hanyar duba tsadar fulawa.

 Shugabar kungiyar Hajiya Fatima Auwalu Yar-Gurasa ta yi wannan kiran a lokacin da ta jagoranci wata zanga-zangar lumana a yankin Chediyar ‘Yan Gurasa da ke karamar hukumar Dala a Kano ranar Juma’a.

‘Yar-Gurasa ta ce tsadar kayayyakin ya zama koma baya ga sana’ar.

Ta bayyana cewa a halin yanzu suna siyan kilo 50 na garin fulawa a kan Naira 40,000 sabanin Naira 17,000 a watannin baya.

“Yawancin mu gwauraye ne, mun dogara da wannan sana’a ne don biyan bukatun ‘ya’yanmu, amma wannan karin kayan masarufi yana jefa rayuwarmu cikin hadari saboda da sana’ar kawai muka dogara.

“Muna kira ga shugaban kasa Tinubu da masu ruwa da tsaki da su kawo mana agaji mu rage farashin kasuwancin mu domin mu samu nasara.

Ta ce idan har lamarin ya ci gaba, ba za a bar su da wani zabi da ya wuce su daina sana’ar ba.

Ta ce, ” Barin sana’ar ba zai yi wa al’umma dadi ba saboda ba za mu samu abin da za mu kula da ‘ya’yanmu ba, kuma hakan zai haifar da yawaitar laifuka da sauran munanan dabi’u.”

“Bari in yi amfani da wannan dama in yi kira ga Abdussamad Isyaku Rabiu da sauran masu ruwa da tsaki da su gaggauta sauya farashin fulawa, ko kuma mu rufe kasuwancin mu.

” Idan muka rufe, ba zai shafe mu, mu kadai ba; hakan zai shafi mutane da dama a jihar nan da ma Arewa baki daya”.

“Muna kira ga masu ruwa da tsaki da su yi abin da ya dace don shawo kan lamarin, domin abin yana kara tabarbarewa. 

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?