Back

Masu PoS ba za su biya haraji na wata-wata ga hukumomi ba, inji Hukumar Kula da Harkokin Kamfanoni

Babban Magatakardar Hukumar Kula da Harkokin Kamfanoni (CAC), Ishaq Magaji, SAN, ya yi ƙarin haske kan koke-koken da masu PoS ke yi na aika harajin wata-wata ga hukumomi bayan rajistar su.

Magatakardar ya bayyana cewa masu PoS za su yi rajista a ƙarƙashin ‘Sunan Kasuwanci’ ne kawai wanda baya buƙatar biyan haraji.

Ku tuna cewa kwanan nan CAC ta umurci masu PoS ko a matsayin wakilai, ‘yan kasuwa ko ɗaiɗaikun mutane, su yi rajista da hukumar kafin fara kasuwanci.

Wannan matakin dai ya sa masu PoS da dama suka nuna rashin amincewarsu da wannan umarni, suna masu cewa rajistar za ta yi tasiri a kan hada-hadarsu da kuma rage ribar da ake samu a kasuwancin tare da hana su aiki.

Magatakardar ya ce: “Idan kuna biyan haraji ga FIRS, to lallai ne ku kamfani mai Limited Liability ne, amma waɗannan za su yi rajistar sunan kasuwanci ne.

“Abin da kawai za a buƙaci su yi shi ne sabunta bayanan su duk shekara da hukumar idan an sami wasu canje-canje.”

Magatakardar ya kuma bayyana cewa a yanzu haka hukumar tana horas da ma’aikatan da zasu rinƙa aiki na awanni 24 domin biyan buƙatun jama’a.

Magaji ya ce za a rufe rajistar masu PoS a ranar 7 ga Yuli, 2024

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?