Back

Masu satar ɗaliban makarantar allo a Sokoto sun buƙaci naira miliyan 20

Makarantar Allon Gidan Bakuso

‘Yan bindigan da suka sace ɗaliban makarantar allo su 16 a jihar Sokoto sun buƙaci a biya su kuɗin fansa naira miliyan 20.

Shugaban makarantar allon, Liman Abubakar ne ya bayyana hakan a ranar Talata.

“Sun kira ni sau biyu da safiyar yau Talata. A cikin kiran farko, sun tambaye ni ko ban damu da halin da ɗalibaina suke ciki ba shi ya sa ban tuntuɓe su ba. Na ce musu ba ni da lambar wayar su.

“Sai suka ce in jira wani kira da misalin ƙarfe 11 na safe. Mintuna kaɗan bayan 11 na safe sai suka sake kira suka umarce ni da in gana da hakimin ƙauyen mu na ce masa ya tara wa yaran naira miliyan 20.

“Na so in roƙe su amma sun ce ba za su rage komai daga kuɗin ba. Na je na tattauna batun da hakimin ƙauyen amma har yanzu ba mu kai ga cimma matsaya ba,” inji shi.

Jaridar ta ruwaito cewa an sace daliban ne a Gidan Bakuso da ke ƙaramar hukumar Gada a ranar Asabar ɗin da ta gabata a lokacin da suke tserewa zuwa azuzuwan su domin gujewa harin da aka kai wa al’ummar.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?