Back

Mataimakin Gwamnan Kano ya nemi gafarar Ribadu bisa zarginsa da hannu a rikicin sarautar jihar

Mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo

Gwamnatin Jihar Kano ta nemi gafarar Mai Baiwa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, bisa zarginsa da hannu a rikicin sarautar da ya ɓarke a jihar.

An ruwaito cewa Mataimakin Gwamnan Jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya zargi NSA da taimaka wa tsohon Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya dawo jihar.

Ribadu dai ya musanta hannu a lamarin inda ya yi barazanar ɗaukar matakin shari’a kan mataimakin gwamnan.

Sai dai Gwarzo ya janye zargin nasa a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidan gwamnati a ranar Lahadi, ya kuma bai wa Ribadu haƙuri.

Ya ce, “Mun ƙara yin bincike kuma muka gano cewa an yaudare mu sosai, kuma a madadin Gwamnatin Jihar muna so mu nemi afuwar NSA.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?