Back

Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda ya kashe kansa a Oyo

Wani Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda da ke aiki da sashin binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sanda da ke Alagbon a jihar Legas, Gbolahan Oyedemi, a ranar Litinin ya kashe kansa a cikin gidansa na kashin kansa da ke mahaifarsa, Ogbomoso, jihar Oyo.

Oyedemi dai ya kasance tsohon mai taimaka wa marigayi tsohon gwamnan jihar, Adebayo Alao-Akala, a tsawon watanni 11 da ya yi yana mulkin dimokraɗiyya a shekarar 2006.

Wata majiya da ke kusa da iyalin ta shaida a ranar Talata a Ibadan, babban birnin jihar, cewa Oyedemi, wanda ya saba ziyartar garinsu a lokacin bukukuwan Ista, ya shaida wa mataimakansa a ƙarshen mako da su je garuruwansu daban-daban don yin bikin tare da yan uwa.

Majiyar ta ce, “Eh, ya kashe kansa. An tsinci gawarsa rataye a gidansa jiya (Litinin). Yana zama shi kaɗai, kuma yakan dawo gida don bikin Ista.

“A wannan karon, ya gaya wa mataimakansa su je su yi biki tare da iyalin su a gidajensu daban-daban. Allah ne kaɗai ya san abin da ya sa shi kashe kansa.”

Duk ƙoƙarin jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Adewale Osifeso, ya ci tura, domin an kasa samun lambar wayarsa.

Jami’in huldɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan FCID, Alagbon, DSP Eguaoje Funmilayo, ya tabbatar da mutuwar Oyedemi.

“A wannan karon, ya gaya wa mataimakansa su je su yi biki tare da iyalinsu a gidajensu daban-daban. Allah ne kaɗai ya san abin da ya sa shi kashe kansa,” inji shi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?