
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, a gidan gwamnatin Kaduna
Mataimakin Shugaban Ƙasar Nijeriya, Kashim Shettima, ya gana da masu ruwa da tsaki na al’ummar Kuriga da ƙaramar hukumar Chikun, ya kuma tabbatar musu da gwamnatin jihar Kaduna cewa za a mayar da malamai da ɗalibai 287 da aka sace a ranar Alhamis a makarantar GSS Kuriga da makarantar firamare ta LEA Kuriga ga iyayen su a raye.
Da yake jawabi a gidan gwamnatin Sir Kashim Ibrahim Kaduna a lokacin da ya kai ziyarar jaje jihar Kaduna a ranar Asabar, Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ce wannan ɗanyen aikin da ya faru ya yi wa Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu ciwo, ya kuma umurce jami’an tsaro da su tabbatar da ceto ɗaliban da malaman daga hannun masu garkuwa, su kuma koma ga iyayensu lafiya.
“Na zo nan ne bisa umarnin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da na ba gwamnati da jama’ar jihar Kaduna haɗin kai kan lamarin da ya faru na sace ɗalibanmu.
“Shugaban Ƙasa ya ji takaicin abin da ya faru kuma ya umarci jami’an tsaro da su mayar da ‘ya’yanmu ga iyayensu,” inji Mataimakin Shugaban.
Ya ƙara da cewa, “Jagoranci yana buƙatar sadaukarwa amma a tabbata cewa Shugaban Ƙasa zai iya aikin. Manufar gwamnati ita ce tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a. An ɗorawa jami’an tsaro baki ɗaya aikin tabbatar da cewa an dawo da yaran lafiya,” inji Shettima.
Mataimakin Shugaban Ƙasan ya nemi kafafen yaɗa labarai da su marawa gwamnati baya a wannan aiki mai wuyar gaske na ganin an sako ‘yan makarantar cikin ƙoshin lafiya ta hanyar kula da rahotanninsu da bayar da rahoto ta yadda ba za su kawo cikas ga dawowar waɗanda aka kama ba.
Gwamna Uba Sani a nasa jawabin ya ce hukumomin gwamnati da na tsaro sun duƙufa wajen ganin an dawo da ɗalibai da malamai lafiya.
“Tun da faruwar lamarin, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, Mataimakin Shugaban Ƙasa, da kuma jami’an tsaro suna aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin jihar Kaduna domin ganin an dawo da yaran lafiya.
“Muna ta aiki tare da al’ummar da ƙaramar hukumar Chikun domin haɗa kai da jami’an tsaro wajen ganin dukkan ɗaliban sun dawo lafiya.
“Dole ne mu tunkari lamarin da dabara ba za mu iya barin kowa ya yi illa ga dawowar yaran lafiya ba. Muna samun ci gaba. Ba za mu faɗi abin da muke yi ba saboda abin da ke da muhimmanci a gare mu shi ne a dawo da yaran lafiya,” inji gwamnan.
Daga baya Mataimakin Shugaban Ƙasa da Gwamna Uba Sani sun shiga wata ganawar sirri da Etsu Gbagyi, sarakunan gargajiya na ƙaramar hukumar Chikun da Kuriga da kuma wasu manyan jami’an gwamnati.