An gama shirye-shirye tsaf domin sa ran ziyartar matar Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu Jihar Kano, inda za ta kaddamar da Ginin Sashen Karatun Lauyoyi da aka sanya wa sunanta a Jami’ar Maryam Abacha da ke Jihar.
Da yake zantawa da manema labarai a Kano, Darakta Janar na yada labaran Gwamna Abba Kabir Yusuf, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana cewa an samar da isassun tsare-tsare na tsaro domin tabbatar da ziyarar ta ta cikin kwanciyar hankali ba tare da cikas ba.
Ya ce gwamnatin jihar tare da rundunar ‘yan sanda sun tsara yadda za a samar da tsaro mai inganci, na haɗin kai ba tare da rudani ba.
Bature ya ce gwamnatin jihar da hukumomin tsaro suna aiki ba dare ba rana domin samar da yanayi na lumana ga maziyartan.
Don haka gwamnati ta yi kira ga mazauna yankin da su gudanar da hada-hadar su ta yau da kullum cikin lumana, kuma su fito, su yi gangami domin tarbar uwargidan shugaban kasar.
A halin da ake ciki, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Muhammad Hussaini Gumel, a ranar Lahadin da ta gabata ya ce, “Mun tara isassun jami’an tsaro da za su bai wa uwargidan mu kariya kafin ziyarar, da lokacin ziyartar da kuma bayan ziyarar.
Ya kara da cewa, “Ba za mu amince da duk wani aiki da zai iya kawo rudani kafin, lokacin, da kuma bayan ziyarar ba.”