An kama wani Abdulazeez Idris, mazaunin Angwan Juma’a da ke ƙaramar hukumar Zariya a Jihar Kaduna, kan zargin sace ‘yar uwarsa ‘yar shekara 6 tare da kashe ta.
Marigayiyar mai suna Aisha Saidu tana kan hanyarta ta zuwa makarantar Islamiyya lokacin da aka sace ta.
An ce ta gane ɗan uwan nata ne wanda shi kuma ya yi amfani da reza ya yanka ta.
Sai dai duk da haka, ya ci gaba da neman kuɗin fansa na naira miliyan 8 ta hannun wani da ba a san ko wane ne ba, wanda ya bayyana kansa a matsayin wanda ya aikata laifin.
A cewar ASP Mansur Hassan, Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘yan Sandan Jihar, lamarin ya faru ne a ranar 12 ga Fabrairu, 2024.
Hassan ya ce mahaifin mamaciyar, Mista Saidu Dahiru na Angwan Juma’a, Zariya, ya sanar da ofishin ‘yan sanda na birnin Zariya cewa ‘yarsa ta ɓace.
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata, ya ce, “An mayar da shari’ar zuwa sashin yaƙi da masu garkuwa da mutane na SCID Kaduna, inda suka gano tare da cafke wanda ya aikata laifin mai suna Abdulazeez Idris a ƙaramar hukumar Maƙarfi.”
“Wanda ake zargin ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa, inda ya amsa laifin kashe yariyar ta hanyar yanka wuyanta da reza saboda ta gane shi sannan ya jefar da gawarta a cikin rijiya.”
Ya kuma bayyana cewa Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, CP Audu Dabigi, ya tabbatar wa jama’a cewa za’a gudanar da bincike mai zurfi a kan lamarin domin tabbatar da adalci ga yarinyar da danginta da suke makoki.
Ya kuma bayyana cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike.