Back

Matashin mawaƙi ya harbe kansa bisa kuskure yayin da yake ɗaukar bidiyo a shafin sada zumunta

Wani matashin mawaƙi ɗan shekara 17 mai suna Rylo Huncho a Amurka ya harbe kansa bisa kuskure yayin da yake ɗaukar wani bidiyo a shafin sada zumunta.

A cikin faifan bidiyon, ya kai bindigar kansa, sannan ya harba.

Rahoton jaridar New York Post ya ce da alamu yaron ya kashe injin kariya na makamin kafin ya harba.

An tsinci gawar matashin a gidansu da ke Suffolk a Jihar Virginia a ranar 15 ga watan Mayu.

Kafin ya mutu, an garzaya da shi Babban Asibitin Sentara Norfolk inda daga baya ya mutu.

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da mutuwar matashin kuma ta ce ya mutu ne sakamakon “harbe kansa da ya yi da bindiga bisa kuskure”.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?