Matatar mai ta Dangote ta fara samarwa kasuwannin cikin gida na Nijeriya da man dizal da kuma man jiragen sama.
Shugaban Ƙungiyar Dillalan Man Fetur Mai Zaman Kanta ta Nijeriya, Abubakar Maigandi, ya bayyana cewa ‘yan kasuwar man ƙasar sun sanya farashin man dizal akan naira 1,225 ($0.96) kan kowace lita bayan sun ƙulla yarjejeniyar siyan mai da yawa, kafin su sanya ribarsu.
Mambobin ƙungiyar suna kula da gidajen mai kusan 150,000 a faɗin Nijeriya, inji Maigandi.
Kungiyar Masu Ƙananan Ma’ajiya da Dillalan Albarkatun Man Fetur ta Nijeriya, ta ce mambobinta na neman takardar lamuni domin sayen man fetur daga hannun Dangote.
“Mambobin mu suna tattaunawa da bankuna kuma wannan tattaunawa ta kai babban mataki. Idan muna da takardun mu na lamuni, za mu fara ɗaukar kayayyakin,” inji babban sakataren ƙungiyar, Femi Adewole.
Wani babban jami’i daga kamfanin da kuma ƙungiyoyin sayar da man fetur daban-daban ya shaida cewa ‘yan kasuwar man na lodin dizal daga matatar mai, wani muhimmin mataki a yunƙurin Nijeriya na samun ‘yancin kai na makamashi.
Bugu da ƙari, Devakumar Edwin, wani babban jami’in kamfani a Dangote, ya tabbatar da cewa kamfanin ya fara rarraba man dizal da man jiragen sama ga kasuwannin cikin gida.
“Muna da adadi mai yawa. Ana kwashe kayayyakin ta ruwa da kuma ta hanya. Jiragen ruwa na yin layi ɗaya bayan ɗaya don lodin man dizal da na jiragen sama. Jiragen ruwa suna ɗaukar mafi ƙarancin lita miliyan 26, kodayake muna ƙoƙarin tura lita miliyan 37 don sauƙin ayyuka,” inji Edwin.