Back

Matawalle ya caccaki dattawan Arewa kan nadamar zaɓen Tinubu

Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle

Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta sha suka kan kalaman da ta yi a kwanakin baya dangane da shugabancin Bola Ahmed Tinubu.

Kwanan nan ne NEF ta ce ta yi nadamar goyon bayan Shugaba Ƙasa Bola Tinubu a zaɓen 2023.

Ƙungiyar ta ce za a ba da fifiko ga wanda ake ganin ya fi kowa shiga tsakani, wanda ba ya jawo yawan cece-kuce, kuma ya fi dacewa da muradun ɗaukacin yankunan ƙasar.

Da yake mayar da martani a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Asabar, Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana matakin da NEF ta ɗauka a matsayin wani nauyi na siyasa ga Arewa.

Matawalle ya jaddada cewa ‘yan ƙungiyar NEF ba su da hurumin yin magana wa ɗaukacin yankin, inda ya ce sun zame wa ‘yan Arewa nauyi a siyasance.

Ya ce, “Hankalina ya karkata ga barazanar da Ƙungiyar Dattawan Arewa ta yi wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wanda abin zargi ne da dolanci.

“NEF ta fi zama nauyin siyasa ga ‘yan Arewa. Ƙungiyar dai na neman tauye haƙƙin wasu ne domin a gane su ko a ɗauke su da muhimmanci a cikin shirin abubuwa duk da gazawar ‘yan takarar da suka ɗauki nauyin su a zaɓen 2023.

Ya yi nuni da cewa NEF ba ta da wani hurumin yi wa Shugaban Ƙasa zagon ƙasa ko barazanar tsige shi.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Dukkanmu mun san Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya lashe zaɓen Shugaban Ƙasa a watan Fabrairun 2023. To, wacece NEF da ke son kawo cikas ga nasarar Shugaban Ƙasa har ma da yi masa barazanar tsige shi?

“Wannan gungun jama’a da gangan sun yi watsi da nauyin da ya rataya a wuyansu na samar da haɗin kai a Arewa ta hanyar nuna godiya ga ƙarin ci gaban da ministocin da Shugaban Ƙasa Tinubu ya naɗa daga Arewa, musamman Arewa maso Yamma ke kawowa Arewa.

“Kungiyar ta NEF ba ta ga ya dace ta nemi ganawa da Shugaban Ƙasa don tattauna batutuwan da suka shafi yankin Arewa ba duk da ɗimbin ƙalubalen da Arewa ke fuskanta kamar yadda Shugaban Ƙasa ya bayyana da kuma magance shi.

“Ƙungiyar har yanzu ba ta ziyarci kowanne daga ministocin da ke aiki kan lamuran tsaro, noma, albarkatun ruwa, harkokin ‘yan sanda, ilimi, lafiya, kasafin kuɗi, harkokin waje, ko kuma wani shugaban hukumomin tsaro a ƙasar nan har ya zuwa yanzu domin sanin abin da ya dace na shirye-shiryen gwamnati da ayyuka.

“Yawancinsu sun fi sha’awar ba wa gwamnati laifi domin a gane su ko a ɗauke su da muhimmanci.

“Shugaba Ƙasa Tinubu a shirye yake ya yi wa Arewa abubuwa da yawa a matsayinsa na Shugaban Nijeriya, al’ummar Nijeriya ne suka zaɓe shi, ba wai wata ƙabila ko wata ƙabila ba, don haka duk wanda ya yi kuskure ya kalli Shugaban Ƙasa Tinubu a matsayin wanda ya gaza ko kuma mai rauni to ya yi kuskure kuma yakamata a sake tunani.

“Irin wannan mutum ko ƙungiya ko dai makaho ne ko kuma bata da damar ganin sabuwar Nijeriya da ta kunno kai. Don haka, furucin NEF na nuna nadamar zaɓen Shugaban Ƙasa Tinubu abin takaici ne. NEF ba ta wuce ƙungiyar da ta ƙi yarda da gaskiya ba kuma tana rayuwa cikin ruɗi.

“Gaskiyar magana ita ce Arewa na alfahari da goyon bayanta ga Shugaban Ƙasa Tinubu kuma za ta ci gaba da alfahari da dangantakarta da Shugaban Ƙasa idan aka yi la’akari da gagarumin sauyi da ci gaban da gwamnatinsa ta kawo wa yankin.”

Matawalle ya yi kira GA NEF da ta ba da fifikon haɗin kai a tsakanin Arewa domin marawa shugabancin Tinubu baya da kuma ƙoƙarin samar da makoma mai ƙarfi da wadata ga Nijeriya.

Ya kuma ja hankalin ‘yan NEF da su sake duba matsayinsu, su mai da hankali kan manufofin bai ɗaya maimakon haifar da ɓaraka a yankin.

“Shawarata ga NEF da sauran su ita ce su goyi bayan gwamnati mai ci su haɗa kai da Shugaban Ƙasa Tinubu domin ciyar da ƙasar gaba,” inji shi.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?