Back

Matsalar abinci: Ƙungiya ta ba da shawarar tura fursunoni noma

Wani jigon ‘Yan Gwagwarmayar Jama’a, Ukwunetu Samuel Ali, ya bayar da shawarar tura fursunoni cikin harkar noma a matsayin magani ga taɓarɓarewar zamantakewa da tattalin arziƙin ƙasa.

Ali ya ba da shawarar ne a cikin wata shawara da ya miƙa wa Gwamnatin Tarayya mai taken: “Tsarin da ya dace na farfaɗo da harkar noma a Nijeriya ta hanyar ɗaukan fursunonin Nijeriya aiki”, da kuma kwafin da aka miƙa wa manema labarai a ranar Juma’a a Lokoja, Kogi State.

Ali shi ne marubucin littafi, mai suna: “A Compendium of Biography of Senator Oluremi Bola Tinubu, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala and Other Notable Women As A Panacea To Engligence Of Girl-Child Education In Nigeria.”

Ali ya lura da tarin albarkatu a ƙasar, da aka bari a ɓarnatar da su tare da illar da ke tattare da hakan a cikin al’umma.

A cewar ɗan gwagwarmayan, buƙata na farko na ɗan Adam abinci ne, kuma hakan ba zai samu ba sai ta hanyar noma, don haka iyawar gwamnati ta mayar da albarkatunta na ɗan adam zuwa noma, zai sa ta samar da al’umma ta gari.

Ya buƙaci gwamnati da ta inganta ƙarfin fursunonin zuwa noma domin wadatar abinci a faɗin ƙasar nan.

Yayin da yake kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi hanzarin yin la’akari da shawararsa, Ali ya ba da tabbacin cewa amincewa da ƙudirin zai magance tagwayen ƙalubalen yunwa da rashin tsaro da ƙasar ke fuskanta.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?