Back

Matsalar tattalin arziƙi: Tinubu ya hana jami’an gwamnati tafiye-tafiyen ƙasashen waje

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya haramtawa ministoci da jami’ai da shugabannin hukumomi tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje da kuɗaɗen jama’a da suke yi.

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ne ya miƙa wannan umarni a wata wasiƙa da ya aikawa Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume.

Wasiƙar ta ambaci “matsalar tattalin arziƙi ta yanzu da kuma buƙatar gudanar da kuɗaɗen shiga yadda ya dace” a matsayin dalilan dakatar da tafiye-tafiyen ƙasashen waje na wucin gadi da kuɗin masu biyan haraji.

Tinubu ya ce waɗanda aka keɓe na buƙatar amincewar Shugaban Ƙasa wanda dole ne a nemi izinin makonni biyu gabanin tafiyar da aka shirya.

Wasiƙar ta ce a wani ɓangare, “Shugaban Ƙasa ya damu da hauhawar farashin tafiye-tafiyen Ma’aikatu, Sassa da Hukumomin Gwamnati (MDAs) da kuma ƙaruwar buƙatar Mambobin Majalisar Zartaswa da shugabannin MDAs su mai da hankali kan wajibcin gudanar da ayyukansu.

“Bisa la’akari da matsalar tattalin arziƙi da ake fama da ita a yanzu da kuma buƙatar gudanar da kuɗaɗen shiga yadda ya dace, na rubuto ne domin in sanar da umarnin Shugaban Ƙasa na sanya dokar wucin gadi na hana tafiye-tafiye ƙasashen waje ga dukkan jami’an gwamnatin tarayya a kowane mataki da kuɗaɗen jama’a na tsawon watanni uku (3) daga Afrilu 2024.

“Wannan matakin na wucin gadi an yi shi ne da nufin rage farashin gudanar da gwamnati ba tare da lalata ayyukan gwamnati ba.

“Duk jami’an gwamnati da suke da niyyar tafiya duk wani balaguro ƙasashen waje da kuɗin jama’a, dole ne su nemi amincewar Shugaban Ƙasa aƙalla makonni biyu (2) kafin wannan tafiya.”

Wannan ci gaban ya biyo bayan wata tafiyar da Ofishin Akanta-Janar na Tarayyar Nijeriya (OAGF) ya yi zuwa ƙasar waje a baya-bayan nan ya haifar da martani.

OAGF ya gudanar da wani taron ƙarawa juna sani kan Gudanar da Kuɗaɗen Jama’a da Daidatacciyar Kulawa da Kuɗaɗen Jama’a na Ƙasa da Ƙasa a birnin Landan na ƙasar Birtaniya.

An gudanar da shi a Otal ɗin Copthorne Tara, Kensington London, tsakanin Maris 4 da Maris 9, 2024.

Taron ya haɗa Kwamishinonin Kuɗi na jihohi da jami’ai daga OAGF.

‘Yan Nijeriya sun bayyana rashin amincewar su kan taron a daidai lokacin da ƙasar ke fama da matsalar canjin kuɗaɗen waje.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?