Back

Matsalar Tsaro: Gwamna Radda yace mazauna Katsina su kare kan su, kada su dogara da gwamnati kawai

Gwamnan jihar Katsina, Umar Dikko Radda, ya buƙaci mazauna jihar da su ɗauki matakin kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga, maimakon dogaro da gwamnati kawai

Gwamnan ya yi wannan kiran ne a ranar Juma’a a gidan gwamnati da ke Katsina yayin da aka yi wani gagarumin taron gaggawa kan tsaro.

Yayin da yake bayyana matsananciyar buƙatar tinkarar matsalar rashin tsaro kai tsaye, ƙarancin abinci, da kuma fatara a cikin jihar, Radda ya jaddada wajibcin ɗaukar matakin gaggawa kan hakan.

Gwamnan yace, “An kira wannan taro ne domin duba yanayin tsaro da kuma ƙaruwar fatara da ƙarancin abinci a cikin jihar.”

“Dole ne mu sake duba yanayin tsaro a jihar mu, mu ɗauki matakin nemo mafita da magance waɗannan ƙalubale. Baya ga rashin tsaro, akwai wasu ƙalubale kamar tashin farashin abinci da yunwa a tsakanin al’umma.” Inji shi 

Ya kara da cewa, “Gwamnati ta shirya tsaf don taimakawa duk al’ummar da ta tsara kanta a yankunan ta, ta hanyar horarwa da samar da kayan aiki.”

Gwamnan ya ce gwamnatin jihar na tunanin kafa kwamitin da zai daƙile tashin farashin abinci da rashin tsaro a jihar.

Ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa gwamnatin jihar za ta yi tunani kuma ta yi aiki da sauri maimakon ta jira tarzomar da ta faru a jihohin Kano da Neja kada ta kai ga jihar Katsina.

Taron ya samu halartar manyan jami’an tsaro, shugabannin ƙungiyoyin tsaro, da manyan sarakunan gargajiya daga Katsina da Daura tare da manyan jami’an gwamnati

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?