Babban Mai Tsawatarwa A Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ali Ndume ya dage cewa mayar da wasu sassan Babban Bankin Najeriya CBN da Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Tarayya FAAN daga Abuja zuwa Legas shawara ce da bata dace ba.
A wata sanarwa da ya sanya wa hannu, Sanatan ya ce, Legas gari ne mai cunkoso sosai. “Ina nan kan baka na game da batun dauke sassan hukumar sufurin jiragen sama FAAN da wasu sassan babban bankin kasar nan CBN zuwa jihar Legas. Idan batun rage cunkoso ne, Jihar Legas ba ta dace ba.”
“Akwai ofisoshin CBN a dukkan jihohin tarayyar. Me ya sa aka mayar da sassan zuwa Legas da ke da yawan jama’a?
“Tun da na shiga tsakanin lamarin mutane ke ta amfani da wata jarida suna kai mani hari suna cewa na tsani Yarbawa. Irin wadannan mutanen masu suka ta jahilai ne kuma ba su san abin da suke faɗa ba.” inji Sanata Ndumi