Back

Mazauna Kebbi sun wawushe ma’ajiyar gwamnati da shagunan ‘yan kasuwa

Wasu mazauna jihar Kebbi sun kai hari wata ma’ajiya na gwamnati da ke unguwar Bayan Kara a Birnin Kebbi, babban birnin jihar a daren ranar Asabar tare da kwashe kayan abinci.

‘Yan ta’addan da suka bijirewa jami’an tsaro da ke ma’ajiyar, sun kuma fasa wasu shaguna da ma’ajiyoyi masu zaman kansu da ke yankin inda suka yi awon gaba da kayan abinci.

Hakazalika sun yi awon gaba da hatsi iri-iri daga wata babbar mota da ta lalace wanda ake son rabawa a Birnin Kebbi.

Wannan dai na faruwa ne a cikin matsalar tsadar rayuwa da aka yi imanin cewa ya samo asali ne sakamakon cire tallafin man fetur da kuma faɗuwar naira.

Shugaban ƙungiyar masu sayar da abinci a Kasuwar Bayan Kara da ke Birnin Kebbi, Muhammadu Gwadangwaji, ya ce wasu matasa ma sun ƙona wasu shaguna da ma’ajiyoyin kayayyakin abinci na ‘yan kasuwa.

“Su (Jami’an tsaro) sun yi ta harbin bindiga da barkonon tsohuwa sama, amma su (matasan) ba su hanu ba. Da ƙarfi suka shiga suka yi awon gaba da ma’ajiyar gwamnati da wasu shagunanmu,” inji shi.

Da yake mayar da martani, Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamna Nasir Idris, Ahmed Idris, ya bayyana lamarin a matsayin “abin takaici”.

Ya ci gaba da cewa: “Tun da farko ‘yan barandan sun kai hari kan kayan abinci da Dangote ya kawo jihar domin rabawa jama’a kafin su je ma’ajiyar gwamnati su yashe.

“Irin wannan lamari bai taɓa faruwa a Kebbi ba. Kayayyakin abincin da suka wawushe na daga cikin kayan abincin da gwamnatin jihar ta siya domin rabawa al’ummar jihar.

Ya kuma ƙara da cewa “Gwamnati ta sawo tare da raba hatsi iri-iri da suka kai sama da naira biliyan 5 a cikin manyan motoci sama da 200. Abin baƙin ciki ne waɗanda suka kutsa cikin ma’ajiyar sun je can ne domin su sace kayayyakin mutanen jihar”.

Ya ce gwamnati ta tsare ma’ajiyar ta domin hana sake afkuwar lamarin.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Nafiu Abubakar, bai amsa kiran wayar da aka yi masa ba kan lamarin.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?