
Ministar Harkokin Mata, Uju Kennedy-Ohanenye
Ministar Harkokin Mata, Uju Kennedy-Ohanenye, ta kai wa Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ƙara tare da neman kotu ta dakatar da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Neja, Abdulmalik Sarkindaji, daga aurar da ‘yan mata marayu 100.
A kwanakin baya ne Kakakin Majalisar ya bayyana shirin aurar da ‘yan matan marayu, waɗanda suka rasa iyayensu a sanadiyyar hare-haren ‘yan bindiga a ƙaramar hukumar Mariga a wani ɓangare na ayyukan mazaɓarsa a ranar 24 ga watan Mayu.
Ya sanar da cewa an ɗauki wannan matakin ne domin “rage wa talakawa raɗaɗin da suke ciki”, inda ya yi alƙawarin biyan sadakin ma’aurata da kuma sayen kayayyakin da za a aurar da su.
Kennedy-Ohanenye, yayin da take zantawa da manema labarai a Abuja ta bayyana shirin a matsayin “wanda ba a yarda da shi ba” tana mai jaddada cewa an fara gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
“Ina so in sanar da mai girma Kakakin Majalisa a jahohin Neja cewa wannan abu ne da Ministar Harkokin Mata ba za ta amince da shi ba, kuma gwamnati ba za ta amince da shi ba.
“Saboda akwai wani abu da ake kira Dokar Kare Haƙƙin Yara kuma na faɗa tun farko, wannan ba wani abu bane kamar yadda aka saba.
“Wajibi ne a yi la’akari da waɗannan yaran, a yi la’akari da makomarsu, a yi la’akari da makomar yaran da za su fito daga cikin aurensu.
“Don haka na garzaya kotu. Na rubuta masa takarda kuma na rubuta takardar koke ga Sufeto-Janar na ‘yan sanda.
“Kuma na ba da umarnin hana shi duk wani abu da yake shirin yi a ranar 24 ga wata, har sai an yi cikakken bincike a kan waɗannan ‘yan matan, a gano ko sun bayar da izininsu, shekarun su, a gano mutanen da za su aure su.” inji ta.
Ministan, yayin da take jaddada buƙatar tabbatar da ilimin ‘ya’ya mata da ƙarfafawa, ta jaddada buƙatar… “Kamar yadda Kakakin bai yi tunanin ƙarfafa waɗannan mata ba ko tura su makaranta ko kuma ba su wani nau’i na horo na kuɗi.”
“Ma’aikatar ta yanke shawarar ɗauka kuma za mu ilmantar da yaran.
“Waɗanda ba sa son zuwa makaranta, za mu horar da su sana’o’i, mu ƙarfafa su don ba wa yarinyar damar gina rayuwarta da kuma yanke shawarar wa za ta aura da kuma lokacin da za ta yi aure.
“Idan saboda wani dalili Kakakin Majalisar ya yi ƙoƙarin yin saɓanin abin da na ambata za a yi Shari’a mai tsanani tsakaninsa da Ma’aikatar Mata ta Tarayya,” inji ta
Ministar ta ƙara jaddada a cikin Dokar Kare Haƙƙin Yara, kowane yaro na ƙasa ne, don haka za a kare haƙƙin kowane yaro daga cutarwa, tashin hankali ko duk wani abu da zai tauye haƙƙinsa.