Back

Ministan al’amuran mata ta yabawa kungiyar injiniyoyi akan zaben mace shugaba 

Ministar Harkokin Mata, Barista (Mrs) Uju Kennedy-Ohanenye, ta yaba wa Ƙungiyar Injiniyoyi ta Nijeriya (NSE) bisa rungumar shirin haɗa kai ta hanyar zaɓen shugaba mace ta farko don ta fara gudanar da harkokin ƙungiyar na tsawon shekaru biyu masu zuwa.

Ministar ta ba da wannan yabon ne a ranar Juma’a lokacin da ‘yan majalisar zartarwa na ƙungiyar, ƙarƙashin jagorancin Shugabar kungiyar, Injiniya (Mrs) Margaret Oguntola, suka kai mata ziyarar ban-girma a ofishinta da ke Abuja.

Ta bayyana cewa zaɓen shugaba mace a karon farko bayan shekaru 66 na kasancewar hukumar tare da shugabanni 34 ya zuwa yanzu, wata manuniya ce ta son haɗa kai da kawo sauyi da zage damtse bisa tsare-tsaren manufofin wannan gwamnati.

Ta ce: “Zaɓen da kuka yi wata babbar alama ce da ke nuna muhimmiyar rawar da mata ke takawa wajen gina ƙasa, don haka dole ne in yaba wa Ƙungiyar Injiniyoyi ta Nijeriya bisa samar da kafa ga mace ta farko da ta yi hidima a cikin wannan muƙami bayan ta samu shugabanni maza 34 a baya.

“Ba mu ɗauki wannan a wasa ba kuma Ma’aikatar Harkokin Mata za ta haɗa kai da ƙungiyar ku don cimma duk burin mu.”

Ministar ta ƙara da cewa wani ɓangare na manufofin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu shi ne inganta samar da abinci tare da bayyana kyakkyawan fatanta na cewa haɗin gwiwa da ƙungiyar zai ƙara ƙarfafa aikin ta hanyar ƙera kayayyakin amfanin gona na gargajiya domin rabawa ga al’ummomin ƙasar nan.

Barista Kennedy-Ohanenye ta ci gaba da cewa shirin ma’aikatar na yin haɗin gwiwa da ƙungiyar ya zama wajibi kamar yadda za ta samar da damarmaki wajen bayar da shawarwari kan Ilimin Sana’a, Fasaha, Injiniya da Lissafi (V-STEM), musamman ga ‘ya’ya mata domin a wayar musu da kai kan samun fasaha da bunƙasuwar kasuwanci.

Ta gode wa shugabannin ƙungiyar bisa wannan ziyarar, sannan ta yi kira ga sauran ƙungiyoyi masu sana’a da su ba da himma, da zummar samar wa mata da yawa dama su ma su bayar da tasu gudunmawar wajen cigaban zamantakewa da tattalin arzikin ƙasa.

Tun da farko, Shugabar Ƙungiyar Injiniyoyi ta Nijeriya, Injiniya (Mrs) Margaret Oguntola, ta bayyana cewa sun zo ma’aikatar ne domin neman ɓangarorin da za su iya yin haɗin gwiwa da ma’aikatar kamar yadda aka umarce su.

Ta yaba wa ministar da kuma Shugaban Ƙasa Tinubu, musamman yadda suka samar da yanayin da zai inganta rayuwar mata a ƙasar nan.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?