Back

Ministan Yaɗa Labarai ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su dawo da kyawawan ɗabi’un da suka rasa

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, yayin Sallar Idi a Kaduna a ranar 10 ga Afrilu, 2024

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su dawo da kyawawan ɗabi’un da suka rasa tare da ci gaba da addu’o’in samun zaman lafiya da ci gaban shugabanninmu da ƙasarmu.

Ya yi wannan kiran ne a Kaduna bayan kammala Sallar Idi.

An gudanar da sallar ne a makarantar Kaduna Capital da ke Kaduna a ranar Laraba 10 ga Afrilu, 2024.

Ministan ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu addu’a, tare da amincewa da ƙoƙarin da yake yi na mayar da Nijeriya cikin ƙasashe mafiya inganci a duniya.

Ya ce: “Ana farfaɗo da tattalin arziƙinmu, kasuwar canjin kuɗaɗen waje na daidaituwa, ana kuma farfaɗo da harkar noma ta yadda za a samu wadatar abinci ga jama’armu, haƙiƙa yanayin tsaron ƙasar nan ma yana inganta.”

Ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi Allah wadai da duk wasu munanan ayyuka da ‘yan ta’adda ke aikatawa, tare da fatan za su tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya sun zauna lafiya.

Idris ya bayyana damuwarsa kan yadda a hankali ɗabi’un ‘yan Nijeriya ke tabarbarewa tsawon shekaru.

Ya kuma yi kira ga dukkaninmu da mu haɗa kai mu dawo da waɗannan ɗabi’u domin farfaɗo da kanmu da kasarmu.

Ya kuma buƙaci matasa da su koyi darasi daga abubuwan da suka faru da dattawan su, kuma su guji biye wa sabbin yayi da duniya ke ciki.

“Nijeriya babbar ƙasa ce; Abin da ya kamata mu yi shi ne, mu haɗa kai mu tabbatar an rungumi dukkan kyawawan ɗabi’u domin amfanin Nijeriya,” inji shi.

Ya ƙara da cewa: “Domin Nijeriya ta sake zama babbar ƙasa, dole ne mu canza ɗabi’unmu kuma mu ci gaba da nuna duk wasu ɗabi’u da muka koya a cikin watan Ramadan.”

Babban limamin masallacin makarantar Capital, Imam Abdurrahman, wanda ya jagoranci sallar, ya gabatar da huɗuba, inda ya yi kira ga musulmi da kiristoci da su tabbatar da cewa Nijeriya ta zauna lafiya da haɗin kai.

Ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su dawo da waɗancan ɗabi’u domin su farfaɗo da ƙasar mu.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?