Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Muhammad Idris, ya ƙaddamar da taron masu magana da yawu, inda ya buƙaci masu magana da yawun su amfana da ilimi, gogewa, da wuraren horaswa da ake da su a yayin taron.
Ministan ya yi magana ne a ranar Alhamis, 1 ga Fabrairu, 2024, a gaban wata tawaga daga Cibiyar Hulɗa da Jama’a ta Najeriya ƙarƙashin jagorancin Farfesa Emmanuel Dandaura, muƙaddashin shugaban Cibiyar.
Ministan ya bayyana rawar da masu magana da yawun suke takawa a matsayin masu tace labarai a kafofinsu daban-daban, “ko a cikin gwamnati, sashi masu zaman kansu, sashen ci gaba, ko kuma sashen sa kai, masu magana da yawun suna da muhimmiyar rawa wajen ƙwato martabar ƙungiyoyinsu da al’umma a cikin dogon lokaci.”
Ya ce hakan ne ya sa ma’aikatar ta haɗa kai da Cibiyar wajen shirya wannan taro.
Ya kuma buƙaci masu magana da yawun da su tuna cewa domin samun nasara a muhimman ayyukan da aka ba su, dole ne su kasance da cikakkun kayan aiki da horarwa da kyawawan ɗabi’u da za su nuna ƙungiyoyinsu da ƙasarsu da kyau.
Ya buƙace su da su ware ranakun 25 – 28 ga Maris, 2024, a kalandarsu domin halartar taron.
Ya yabawa wannan shiri kuma ya ce yana zuwa a lokacin da ya dace da gwamnati za ta inganta Yarjejeniyar Ƙimar Ƙasa.
Ya ba da tabbacin cewa masu magana da yawun za su ɗauki saƙon, su yi amfani da shi, sannan su yaɗa shi ta hanyar dandalinsu.