A ranar Alhamis ne Ministar Harkokin Mata, Uju Kennedy-Ohanenye, ta bayyana bayar da tallafin karatu tare da kyaututtuka daban-daban ga ‘yan mata marayu 100 a Jihar Neja, gabanin ɗaurin aurensu a yau Juma’a.
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Abdulmalik Sarkindaji, ne ya ɗauki nauyin ɗaurin auren.
A baya Ministar ta caccaki auren ‘yan matan, inda ta ce hakan ya saɓa wa dokar kare haƙƙin yara.
Kennedy-Ohanenye, wacce ta bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja, ta bayyana cewa ta roƙi Sufeto-Janar na ‘Yan Sandan Ƙasar da ya dakatar da ɗaurin auren, inda ta ƙara da cewa ita ma ta shigar da ƙara a kotu tana neman a ba da umarnin hana Kakakin Majalisar gudanar da ɗaurin auren ‘yan matan marayu.
Da yake mayar da martani, Kakakin Majalisar ya caccaki Ministar kan yadda ta tsunduma cikin wani lamari na addini da al’ada da ba ta fahimta ba.
Gabanin ɗaurin auren, Ministar wadda Mataimakiyar ta ta Musamman, Adaji Usman, ta wakilta, ta je Neja domin sanar da bayar da tallafin karatu ga ‘yan matan da kuma ba su wasu kayayyaki, da suka haɗa da zannuwa da kayan abinci.
An raba kayayyakin ne ga ‘yan matan 100 a Fadar Sarkin Kontagora, Mohammed Muazu.
Ministar, ta hannun Usman, ta gabatar da na’urar PoS 10, zannuwa 100 da buhunan shinkafa 10kg 350.
Ta sanar da bayar da tallafin karatu zuwa matakin jami’a ga duk ‘yan matan da ke son zuwa makaranta.
Har ila yau, Sarkin Kontagora ya sanar da bayar da tallafin keken ɗinki ga kowacce daga ‘yan matan.
Kennedy-Ohanenye ta kuma bayar da umarnin a buɗe asusun ajiyar banki ga dukkan matan 100 da za a biya su kuɗaɗen alawus na tsawon watanni shida masu zuwa don samun damar tarewa a gidajen mazajensu.
Ta zargi kafafen yaɗa labarai da ta’azzara cece-ku-ce kan auren marayun 100, inda ta ce “Ban yi niyyar dakatar da auren ba, sai dai in tabbatar da ko ‘yan matan sun kai shekarun aure kuma ba a tilasta musu yin auren ba.”