Ministar Harkokin Mata, Uju Kennedy -Ohanenye, ta janye ƙarar da ta shigar a baya a kan Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Neja, Abdulmalik Sarkindaji, bayan ya yanke shawarar aurar da mata marayu 100 daga mazaɓarsa.
Da take zantawa da manema labarai, Ministar ta bayyana cewa, ma’aikatar tare da haɗin gwiwar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Neja, da kuma sarakuna daga jihar, a halin yanzu suna gudanar da bincike kan shekarun ‘yan matan domin sanin ko sun kai shekarun da aka ƙayyade na aure.
A cewarta, a yanzu Ma’aikatar Harkokin Mata za ta mayar da hankali wajen ƙarfafa ‘yan matan, da ma sauran waɗanda rashin tsaro ya shafa a jihar.
A makon da ya gabata ne Shugaban Majalisar, Sarkindaji, ya bayyana shirin aurar da mata marayu 100 a mazaɓarsa a wani mataki na rage raɗaɗin da suke ciki.
Yayin da lamarin ya haifar da cece-ku-ce a ƙasar, Ƙungiyar Kare Haƙƙin Musulmi (MURIC), ta buƙaci Ministar da ta janye ƙarar da ta rubuta wa Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda.
Shugaban Ƙungiyar MURIC, reshen Jihar Kano, Malam Hassan Indabawa, wanda ya yi wannan kiran a daren ranar Alhamis cikin wata sanarwa, ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su koyi mutunta al’adun juna.
“Mun gano hukunci mai tsanani da gaggawa da mai girma Ministar Harkokin Mata ta ɗauka kan wani al’amari da ya wuce hurumin ma’aikatarta.
“Ƙoƙarin da ministar ta yi na amfani da kafafen yaɗa labarai wajen lalata shirin auren ‘ya’ya mata marasa galihu da marayu 100, waɗanda suka samu rauni saboda rashin iyayensu biyu sakamakon mummunar ta’addanci da tada ƙayar baya, ya fallasa jahilcinta ga al’adun Musulmin Arewa.
Indabawa ya ƙara da cewa: “MURIC ta lura da cewa an yi shi ne da gangan don murza ra’ayin jama’a game da batun auren, da kuma yunƙurin tozarta Sarkin-Daji, bayan ya nuna matuƙar damuwarsa ga buƙatun ‘yan mazaɓarsa.”
An shirya ɗaurin auren ne a ranar 24 ga Mayu, 2024.