Back

Ministar Harkokin Mata ta musanta janye ƙarar Kakakin Majalisar Dokokin Neja kan aurar da mata marayu

Ministar Harkokin Mata, Uju Kennedy-Ohanenye

Ministar Harkokin Mata, Uju Kennedy-Ohanaeze, ta ce za a ƙarfafa ‘yan mata marayu da aka shirya aurar dasu a jihar Neja.

Yayin da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Neja, Abdulmalik Sarkindaji ya ba da shawarar aurar da mata marayu 100 a mazaɓarsa, Ministar ta kai shi kotu kan lamarin.

“Waɗanda suka gama karatun sakandare, za su iya shiga buɗaɗɗiyar jami’a yayin da suke sana’a ko kuma mu samar musu aiki yayin da suke kasuwanci da zuwa makaranta,” inji ta a shirin Siyasa A Yau na ranar Juma’a na Gidan Talabijin na Channels.

“Sannan waɗanda ba su gama sakandare ba za su koma makaranta su kammala. Wannan wani abu ne da zai dace da su: zuwa buɗaɗɗiyar jami’a da kuma samun abin yi. Kamar PoS, waɗanda suka gama karatun sakandare kuma suna da shekaru 18, za mu iya ba su damar fara samun kuɗi yayin da suke zuwa makaranta.”

Ta kuma bayyana cewa har yanzu ba a janye ƙarar da ke ƙalubalantar aurar da matan ba.

“Har yanzu ba a janye ƙarar ba. Ina so in bayyana hakan. Ta yaya zan janye ƙarar a rana guda?”

“To, kafin ma in janye ƙarar, sai mun koma kotu sannan mu shaida wa kotu cewa mun sasanta. Za mu janye ƙarar. Kun gane?

“Ta yaya zan je in janye? Har yanzu muna ƙoƙarin tsara kanmu kan yadda za mu haɗa kai da kyau da kuma magance wannan matsalar.”

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?