Tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Kingsley Moghalu, ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu kan matakin da ya ɗauka na cire tallafin man fetur da gyaran canjin kuɗi.
Moghalu, wanda ya nuna damuwarsa kan yawan ‘yan siyasa a wannan gwamnati, ya buƙaci shugaban ƙasar da ya yi wa majalisar ministocinsa garambawul a cikin shekarar farko ta gwamnatinsa.
Ya yi magana ne a karo na 16 na babban taro da bayar da kyaututtuka na jaridar Leadership na 2023 da aka gudanar a otal ɗin Transcorp Hilton, Abuja.
Ɗan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar Young Progressive Party (YPP) a zaɓen 2019 ya kuma buƙaci shugaban ƙasar da ya kafa tawagar tattalin arziƙi mai mutane bakwai da ta ƙunshi masana tattalin arziƙi kawai.
Moghalu, wanda ya gabatar da wata muhimmiyar takarda mai taken “Tattalin arziƙin Nijeriya da ke cikin mawuyacin hali, menene mafita”, ya ce hakan ya zama dole idan ana so ƙasar ta fita daga halin da take ciki.
Ya kuma yaba da matakin da CBN ya ɗauka a halin yanzu na ƙara tsaurara rashin samun tsabar ƙudi.
Ko da yake an jinkirta, ya ce ya zama dole idan aka yi la’akari da irin hare-haren da gwamnatin da ta gabata ta kai wa bankin.