Wani mutum da har yanzu ba a gano wanene shi ba tare da abokinsa sun yi mummunan hatsari a gadar Berger da ke Abuja ranar Alhamis.
An tattaro cewa wata mota ƙirar Toyota Camry da suke ciki ta faɗo daga kan gadar da misalin ƙarfe 3:10 na rana.
Motar mai lamba ABJ 135 HF, ta fito ne daga yankin Area 1 na babban birnin ƙasar, lokacin da ɗaya daga cikin tayoyin ta ya fashe, wanda hakan ya sa direban ya kasa shawo kan motar.
“Ina nan tare da abokina sai motar ta faɗo daga kan gadar da gudu; tare da taimakon sauran mutanen da ke kusa da mu, mun samu nasarar kuɓutar da su, bayan nan aka kai su asibiti.”