Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa kafafen yaɗa labarai wani babban ginshiƙi ne na haɓaka muhalli tare da kare martabar mulkin dimokiraɗiyya.
Ministan ya faɗi haka ne a lokacin bikin ba shi lambar yabo a wani ɓangare na Ranar ‘Yancin Aikin Jarida wanda aka yi a Abuja.
Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya (NUJ) ita ce ta karrama shi da lambar.
A jawabin sa jim kaɗan bayan ya karɓi lambar, Idris ya bayyana farin ciki da karramawar, musamman ganin ayyukan da ya yi da muƙaman da ya riƙe a fagen aikin jarida kafin a naɗa shi minista.
Ya ce: “Wannan karramawa ta yi min sosai, wanda ke da muhimmanci a kai na da kuma gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR.
“Wannan kyakkyawan karimcin zai zaburar da ni na sake sadaukar da kai ga hidimar al’ummar mu mai girma da kuma bil’adama baki ɗaya.”
Da yake magana kan taken bana na Ranar ‘Yancin Aikin Jarida, wato “Jarida ta Duniya: Aikin Jarida a Yayin da ake Fuskantar Matsalar Muhalli,” sai ministan ya ce, “A yayin da ake fuskantar matsalar muhalli, ’yan jarida sun kasance masu kula da gaskiya da kuma masu fafutikar tabbatar da gaskiya. Suna ƙarin haske kan rashin adalci na muhalli, suna fallasa ayyukan da ba daidai ba, da kuma ɗaga muryar waɗanda lalacewar muhalli ta fi shafa. Ta hanyar rahoton binciken su, suna ɗaukar gwamnatoci da ƙungiyoyin kamfanoni alhakin ayyukan su da bayar da shawarar manufofin da ke haɓaka ɗorewa da kiyaye duniyar mu.
“Taken taron na bana ya yi tasiri sosai kan manufofin ma’aikatar mu da kuma batutuwan da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sa a gaba, waɗanda suka haɗa da maido da amana, sake daidaita ƙimar ƙasa, da samar da yanayi mai kyau ga kafafen yaɗa labarai. Ya jaddada muhimmancin aikin jarida wajen magance matsalar muhalli.”
Ya ƙara da cewa, “A cikin tarihi, kafofin watsa labarai, a matsayin masu kula da gaskiya kuma masu samar da sauyi na zamantakewa, sun yi tsayin daka don yin la’akari, suna shawagi a kan ayyukan mutane, gwamnatoci, da kamfanoni.
“A wannan lokaci na rikicin muhalli, aikin watsa labarai ya wuce bayar da rahoto kawai; ya na ƙunshe ne da sadaukar da kai don shirya ayyukan gama-gari don amfanin jama’a. Tare da ikon faɗakarwa, ilmantarwa, da zaburarwa, kafofin watsa labarai su na da ikon da ba zai misaltu ba don kunna motsi, ɗaukaka muryoyi, da haifar da canjin ɗabi’a ga muhalli.”
Bugu da ƙari, Idris ya ce, “Yayin da mu ke bikin Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida ta Duniya, dole ne mu yi tunani a kan muhimmancin kafafen watsa labarai masu ‘yanci don bunƙasa mulkin dimokiraɗiyya, inganta gaskiya, da kuma kare haƙƙin bil’adama.
“Aikin jarida ya zama ginshiƙin tsarin dimokiraɗiyya ta hanyar samar da muhimmin dandali na yaɗa labarai, musayar ra’ayi, da kuma ɗora wa masu riƙe da madafun iko alhakin su.
“Kafafen yaɗa labarai na Nijeriya sun kasance masu fafutikar tabbatar da ɗorewar mulkin dimokiraɗiyya a ƙasar nan, kuma a irin wannan lokaci, mu na jinjina wa jajircewa da sadaukarwar ku kan aikin jarida.
“Duk da haka, yayin da mu ke murnar gudunmawar da ‘yan jarida ke bayarwa ga al’umma, mun kuma yarda da ƙalubalen da ‘yan jarida ke fuskanta wajen gudanar da muhimman ayyukan su. A matsayin su na masu kare muhalli, ‘yan jarida su kan fuskanci barazana, tsangwama, da tashin hankali saboda jajircewar su wajen fallasa laifukan muhalli da kare duniyar mu.”
Dangane da Ranar ‘Yancin ‘Yan Jarida ta Duniya, ministan ya ce dole ne mu sake jaddada aniyar mu ta kare haƙƙin ‘yan jarida da tabbatar da tsaron su.
“A matsayi na na Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, ina so in ƙara jaddada aniyar mu ta kare ‘yancin aikin jarida, inganta ra’ayoyi mabambanta, da kare haƙƙin ‘yan jarida.
“Mu ƙara zage damtse wajen gina makoma inda aikin jarida zai bunƙasa, a tabbatar da ‘yancin ‘yan jarida, da kuma kare duniyar mu har zuwa al’ummomi masu zuwa.
“Yayin da mu ke gudanar da ayyukan mu, dole ne mu kuma tuna cewa Nijeriya, muhallin mu, ita ce abin da ya kamata mu fara karewa daga labaran ƙarya.”