
Shugaban NAHCON, Malam Jalal Ahmad Arabi
Hukumar Alhazai ta Nijeriya, NAHCON, ta ce tana ƙoƙarin magance ƙalubalen da Musulman Nijeriya ke fuskanta na neman bizar Umrah na tafiya ƙasar Saudiyya a cikin watan Ramadan.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Mataimakiyar Daraktar Hulɗa da Jama’a ta NAHCON, Hajiya Fatima Sanda Usara, ta bayyana lamarin a matsayin abin takaici.
Ta ce, “Ƙalubalen da Musulman Nijeriya ke fuskanta a halin yanzu na samun bizar Umrah na tafiya Saudiyya a watan Ramadan, abin takaici ne matuƙa, kuma ya samo asali ne daga yadda ake amfani da damar da aka bayar ta hanyar da bata dace ba wajen ba da bizar.
“Akwai keɓaɓɓen adadin bizar Umrah da ake ware wa ƙasashe kuma bizar Umrah na Ramadan yawanci ya fi tsada.
“A baya-bayan nan, Masarautar Saudiyya ta tsawaita wa’adin bizar zuwa kwanaki 90. A bayyane yake cewa da yawa daga cikin ‘yan Nijeriya sun sami waɗannan biza ne a kan farashi mai rahusa a wasu lokutan, ba shakka da sa ran gudanar da aikin Umrah a watan Ramadan tare da su.
“Waɗannan mutane sun yi amfani da tsawaita wa’adin bizar ta hanyar tsawaita zamansu a masarautar ko kuma riƙe biza ba tare da amfani da su ba har zuwa watan Ramadan, wanda hakan ya haifar da ƙarancin biza ga sauran ‘yan Nijeriya.
“Yawan neman bizar Umrah a watan Ramadan yana ƙara ta’azzara wannan ƙarancin, wanda hakan ya sa ‘yan Nijeriya da dama ba su iya sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na addini. Ya zuwa yanzu, biza kaɗan ne ke raguwa lokaci-lokaci bisa yawan ‘yan Nijeriya da ke bayar da guri ta hanyar tashi daga Saudiyya, amma biyan kuɗin waɗannan guraren caca ne don haka ana shawartar mahajjata masu ƙaramin ƙarfi da su kasance masu hikima”.
Sai dai ta bayyana cewa Jami’in Hulɗa da Jama’a na NAHCON na Saudiyya ya tattauna da ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya kan lamarin.
“Duk da cewa tattaunawar ta kasance mai ma’ana, amma ya tabbatar da cewa rabon bizar yana bin tsarin na’ura mai kwakwalwa,” inji ta.
“Bugu da ƙari, NAHCON ta rubuta wasiƙa a hukumance inda take isar da damuwar ta kai tsaye ga ƙasar Saudiyya, inda ta bayyana illolin rashin samun biza ga Masu Gudanar da Tafiya na Nijeriya.
“Bugu da ƙari, Shugaban Hukumar NAHCON, Malam Jalal Ahmad Arabi, ya ziyarci ofishin jakadancin Saudiyya da ke Nijeriya da kan sa, domin lalubo hanyoyin magance wannan matsala.
“Muna so mu tabbatar wa dukkan masu sha’awar aikin Umrah na Nijeriya cewa NAHCON tana jajircewa wajen ganin an shawo kan lamarin.
“NAHCON za ta ci gaba da yin aiki ba tare da gajiyawa ba tare da haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki don samun gamsasshen maslaha ga rashin samun bizar.”