
Hukumar gidan gyaran hali ta jihar Kano ta yi watsi da rahotannin da ke cewa wata fitacciyar ‘yar Tiktok Murja Ibrahim Kunya ta tsere daga daga hannuwan su.
Hukumar ta yi gaggawar bayyana cewa an saki Murja Ibrahim Kunya ne bisa umarnin wata babbar kotun jihar.
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, da hukumar ‘yan sandan Shari’a ta Jihar Kano, sun bayyana cewa tana neman Murja Kunya da wasu mutane guda biyar, inda hukumar ta kama ta a unguwar Hotoro Tinshama da ke cikin birnin Kano a karshen makon jiya.
An kama ta ne bisa korafin da makwabtan ta suka yi kan rashin da’a da ta yi wanda ya hada da lalata da jama’a, yunkurin cin hanci da rashawa da daukar ‘yan mata karuwanci da kuma yada labaran karya da kalaman batanci a shafukan sada zumunta.
Bayan kama ta, an gurfanar da ita a wata kotun shari’a da ke unguwar Gama a birnin, inda alkalin kotun, Malam Nura Yusuf Ahmed, ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare ta a gidan gyaran hali har zuwa ranar Talata ashirin ga watan nan domin sauraron bukatar belin ta.
An tsare Kunya ne bayan ta musanta tuhumar da mai gabatar da kara, Aliyu Abideen ya karanta mata.
Sai dai a ranar Lahadin da ta wuce kwanaki biyu da dage zaman, rahotanni sun bayyana cewa ta bace daga gidan yarin, lamarin da ya sa aka fara hasashe kan ko ta tsere ne.
Sai dai mai magana da yawun gidan yari na Kano, Musbahu Kofar Nasarawa, ya ce Murja Kunya ba ta kubuta daga inda ake tsare da ita ba, ya ce, kotun da ta tsare ta ita ta sake tunda dama ajiyar ta aka ba su.
Musbahu ya ce an saki Murja ne tun ranar Alhamis, wanda ke nufin ta shafe kwanaki biyu a tsare maimakon bakwai.
“Kotu ce ta kawo mana ita domin a ci gaba da tsare ta, kuma kotun ce ta ce mu sake ta,” inji shi