Mutane 19 ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya afku a yankin Okene na Jihar Kogi, kamar yadda Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta bayyana a ranar Lahadi.
“Tawagar agajin gaggawa na FRSC sun jure sama da sa’o’i uku na wuta a ƙoƙarinsu na ceto waɗanda mummunan hatsarin ya rutsa da su wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 19 a ranar Lahadi 28 ga Afrilu, 2024 a Okene bypass, kan babban titin Okene-Lokoja a Jihar Kogi,” inji Jami’in Kula da Harkokin Ilimi na Hukumar FRSC, Jonas Agwu, a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
Ya ƙara da cewa, hatsarin ya haɗa da motoci biyu, da babbar mota, da kuma wata motar bas ƙirar Toyota Hiace daga Jihar Kano, waɗanda suka ci karo da juna.
Sanarwar ta ƙara da cewa “Tasirin karon ya haifar da gobarar da ta ƙona waɗanda lamarin ya shafa har lahira.”
Mutane 22, dukkansu maza ne hatsarin ya rutsa da su. Amma 19 daga cikinsu sun mutu sannan ɗaya ya samu rauni. Jami’an FRSC sun ceto sauran mutane biyun ba tare da wani rauni ba.
An ajiye gawarwakin waɗanda suka mutu a Babban Asibitin Okene.