Wasu mazauna garin Takum da ke Jihar Taraba guda uku sun rasa rayukansu sakamakon wata iska mai tsanani da ta afkawa yankin har sau biyu cikin kwanaki biyu.
Lamarin na farko a cewar wani mazaunin garin, Malam Maiwada Takum, ya auku ne da yammacin ranar Talata, inda ya yi ɓarna mai yawa ga gine-ginen gidaje, kasuwanci, makarantu da ofisoshi.
Takum ya ce da farko yanayin ya kawo ruwan sama mai yawa, sannan aka yi wata iska mai ƙarfi wadda ta ɗauki sama da sa’a ɗaya da rabi.
“Tasirin ya yi muni, inda wasu gine-gine suka ruguje sannan mutane da dama suka maƙale. Ɓarɓashin gine-ginen da ke yawo a iskar, ya raunata mazauna da yawa,” inji shi.
Wani mazaunin garin, Yakubu Adamu, ya ce guguwar da ta yi ɓarna sosai ga dukiya da ababen more rayuwa, baya ga asarar rayuka.
Ya ce an tabbatar da mutuwar mutane uku, sannan wasu da dama sun samu raunuka.
Ya ƙara da cewa “Adadin waɗanda suka mutu da waɗanda suka raunata na iya ƙaruwa yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin ceto mutane.”
James Gangum ya buƙaci agajin gaggawa daga gwamnatin jihar da Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa (Nema) domin tallafawa waɗanda iftila’in ya shafa.
A ranar Laraba kuma, wata iska mai ƙarfi ta sake afkawa garin Takum, wacce ta ƙara lalata gine-gine tare da raunata mutane da dama.
Guguwar mai ɗauke da ruwan sama mai ƙarfin gaske ta faro ne jim kaɗan bayan da Gwamna Agbu Kefas ya shiga garin domin duba irin ɓarnar da guguwar ta yi a ranar Talata da yamma.
An ruwaito cewa guguwar wadda ta faro da misalin ƙarfe 2:30 na yammacin ranar Laraba, ta yi sanadiyyar lalata gine-gine da dama da suka haɗa da gidajen zama, makarantu, sandunan wutar lantarki, da bishiyoyi.
Lamarin na biyu ya kawo cikas ga ƙoƙarin gwamnan na tantance ɓarnar da guguwar ta yi a ranar da ta gabata.
Mista Emmanuel Bello, Babban Mai Taimaka wa Gwamna Agbu Kefas kan Harkokin Yaɗa Labarai da Sadarwa na Zamani, ya ce gwamnan ya shiga Takum ne domin duba irin ɓarnar da iska ta yi, kuma garin ya sake samun ruwan sama mai yawa.
Hakazalika, an ba da rahoton mutuwar mutum ɗaya tare da raunata wasu da dama sakamakon wata iska da ta lalata gidaje sama da 100 a unguwar Agbashi da ke ƙaramar hukumar Doma a jihar Nasarawa.
Mataimakin Shugaban ƙaramar hukumar Doma, John Bako-Ari, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata.
A cewar Bako-Ari, guguwar ta yi ɓarna matuƙa, da suka haɗa da lalata gidaje sama da 100, masallacin Agbashi Central, wani ɓangare na makarantar Pilot Primary School Agbashi, da dai sauran kayayyakin more rayuwa na jama’a.
Mista Anthony Oshinyeka, Shugaban Riƙo na Ƙungiyar Ci Gaban Agbashi (ADA), ya bayyana alhininsa game da lamarin da kuma mummunar illa ga matsugunan Bassa a Iponu, inda mutum ɗaya ya mutu, wasu bakwai kuma suka raunata.
Oshinyeka ya yi kira da gwamnati ta sa baki cikin gaggawa domin taimakawa mazauna yankin da abin ya shafa.
Ya kuma buƙaci a gaggauta sakin kayan agaji da taimakon magani daga gwamnati da masu hannu da shuni don tallafawa al’ummomin da abin ya shafa.