Back

Mutane 45 sun mutu yayin da wata baƙuwar cuta ta addabi al’ummar Kano

Kimanin mutane 45 ne aka ruwaito sun rasa rayukansu sakamakon ɓarkewar wata baƙuwar cuta a ƙauyen Gundutse da ke ƙaramar hukumar Kura a Jihar Kano.

An ruwaito cewa waɗanda lamarin ya rutsa da su, galibinsu mata, yara, da kuma tsofaffi, sun nuna alamun cutar zazzaɓin cizon sauro, gudawa, da amai.

Mazauna yankin sun bayyana damuwarsu game da ƙaruwar mace-macen ba zato ba tsammani a cikin makonni biyun da suka gabata, inda da farko suka danganta su da cututtukan da aka saba.

Sai dai lamarin ya zama mai firgitarwa yayin da al’ummar suka fara binne mutane biyar a kullum, lamarin da ke nuni da cewa an samu babbar matsalar rashin lafiya.

Abu Sani, wani mazaunin garin da ya rasa ‘ya’ya biyu, ya ce da farko iyalinsa sun yi tunanin cutar zazzaɓin cizon sauro ce ke damun ɗansa ɗan shekara biyu, wanda ya rasu duk da taimakon likitoci.

Ya ce bayan mako guda, wani ɗan ya suma sannan kuma ya rasu kafin a kai shi asibiti.

Wata mazauniya mai suna Hajara Abubakar, wadda ta kai ɗanta wani asibitin yankin domin yi masa magani, ta ce, “Sama da makonni biyu mutane ke mutuwa a nan sakamakon cutar da ba mu sani ba. Ya zuwa yanzu, na san mutane 40 da suka mutu.”

Jami’an lafiya a asibitin na Gundutse sun shaida cewa kawo yanzu an samu rahoton mutuwar mutane 20.

Ɗaya daga cikin ma’aikatan lafiya a asibitin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce tuni sun kai rahoton faruwar lamarin ga Ma’aikatar Lafiya ta Jihar kuma an tattara ruwa da jini don a auna su a ɗakin gwaje-gwaje domin sanin ainihin musabbabin ɓarkewar cutar.

Yayin da mazauna ƙauyen ke dakon sakamakon gwajin, suna hasashen cewa rashin tsaftar muhalli a ƙauyen Gundutse na iya taimakawa.

Domin yin taka tsan-tsan, majalisar ƙaramar hukumar ta rufe rijiyar burtsatse guda ɗaya, lamarin da ya sa mazauna yankin yin amfani da ruwan rijiya.

Shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Kura, Yahaya Tijjani Kura, ya tabbatar da cutar amma ya musanta adadin waɗanda suka mutu, inda ya ce yara uku ne kawai suka rasu.

Sai dai kansila mai wakiltar Gundutse, Dauda Abdulhamid Gundutse, ya bayyana mutuwar yara uku zuwa biyar da kuma ci gaba da yi wa wasu da abin ya shafa magani.

Duk da rahotanni masu karo da juna, an gano sabbin ƙaburbura guda 35 da suka haɗa da na ƙananan yara guda shida a ziyarar da aka kai maƙabartar tare da wasu mutanen yankin, wanda ya saɓawa adadin da hukumomin yankin suka bayar.

Da aka tuntuɓi Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, Abubakar Labaran Yusuf, ya ce har yanzu bai samu rahoton hukuma daga jami’an lafiya na ƙananan hukumomin ba amma ya ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano ainihin musabbabin mace-macen.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?