Back

Mutanen ƙauye sun gudu yayin da ‘yan bindiga suka addabi al’ummomi 10 a Kaduna

Mazauna unguwanni 10 a ƙaramar hukumar Giwa ta Jihar Kaduna sun bar gidajensu sakamakon ayyukan ‘yan bindiga a yankin.

An gano cewa da yawa daga cikin waɗanda lamarin ya shafa musamman mata da ƙananan yara sun yi tattaki mai nisa domin neman mafaka a babban garin na Giwa.

Umar Auwal Bijimi, wakilin mazaɓar Giwa ta Yamma a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, ya shaida a jiya cewa, an fara gudun hijirar ne bayan korar wani jami’in soja mai ƙwazo kuma ƙwararre mai suna Sajan Usman Hamisu Bagobiri, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen yaƙar ‘yan bindigan da suka addabi yankin.

Ya ce rashin Sajan Bagobiri ya baiwa ‘yan ta’addan ƙwarin guiwa, lamarin da ya sa munanan ayyukan da suke yi suka ƙaru tare da tarwatsa mazauna ƙauyukan.

Bijimi ya ce ƙauyukan da lamarin ya shafa sun haɗa da Gogi, Angwar Bako, Marge, Tunburku, Bataro, Kayawa da Yuna.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da hukumomin soji da su maido da Sajan Bagobiri bakin aiki tare da tura ƙarin sojoji masu jajircewa don ci gaba da yaƙi da ‘yan bindigar, ta yadda za a tabbatar da tsaron mutanen ƙauyukan da ba su ji ba ba su gani ba, tare da ba su damar ci gaba da ayyukan noma.

Korau Fatika, wani mazaunin garin, ya tabbatar da labarin Bijimi, inda ya bayyana cewa hare-haren ‘yan bindiga da ake ci gaba da kai wa mutanen ƙauyen ya sanya su ka gudu da iyalansu.

Ya koka da yadda ake samun yawaitar sace-sacen mutane musamman mata, lamarin da ya sa mazauna ƙauyukan barin gidajensu.

Nuhu Lawal Umar Hakimin Fatika ya yi kira da a samar da tsaro a yankin inda ya jaddada matuƙar buƙatar gwamnati ta shiga tsakani.

Samuel Aruwan, Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida ya ce masu ruwa da tsaki da suka haɗa da Shugaban Ƙaramar Hukumar Giwa, Alhaji Abubakar Shehu Giwa, da shugabannin ƙaramar hukumar sun tattauna da ma’aikatar dangane da matsalar tsaro.

Ya tabbatar da cewa lamarin ya kai ga hukumomin da suka dace, kuma ana ci gaba da haɗin gwiwa don inganta tattara bayanan sirri da kuma ƙarfafa matakan tsaro a cikin al’ummomin da abin ya shafa.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?