Back

Mutum daya ya rasa ransa a yayin da ‘yan sanda ke jajantawa iyalan wanda abin ya shafa

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana matukar alhinin ta dangane da rasuwar dan shekaru ashirin da biyar, Ismail Yunusa, wanda ake zaton hayakin tiya gas ne ya shaka, yayi masa illa a lokacin da ‘yan sanda ke kokarin kwantar da tarzoma a ranar Lahadin da ta gabata a unguwar sheka da ke cikin garin Kano.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa an garzaya da marigayin asibitin koyarwa na Aminu Kano, inda ya rasu a lokacin da yi mishi magani.

Kiyawa ya ce ‘yan sanda “na mika ta’aziyya ga ‘yan uwa da abokanan marigayin.”

Lamarin dai ya bayyana ne a lokacin da wani Mohammed Rabiu, ya Kai wa ‘yan sandan yankin Ƙarar wani Abba Mohammed dukkan su mazauna yankin unguwar Sheka Dandurumi wanda yace shi da abokan shi ne suka yi mishi duka jina-jina da munanan raunuka.

Kiyawa ya bayyana cewa, an tattara jami’an ‘yan sanda tare da tura su wurin da lamarin ya faru domin tarwatsa Wadanda Ake Zargi da aika-aikan tare da kama su, “Abin takaici, ‘sai suka yi wa tawagar ‘yan sanda farmaki tare da jifan su da duwatsu da yin amfani da muggan makamai.

“A cikin gaggawar mayar da martani da kuma hana al’amarin ya rikice zuwa tashin hankali, ‘yan sanda amfani da hayaki mai sa hawaye, cikin hikima, suka tarwatsa taron yayi da suka maido da zaman lafiya.”

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Muhammad Hussaini Gumel ya bukaci jama’a da su kwantar da hankulan su tare da kauce tada kayar baya ga jami’an tsaro da suka kuduri aniyar yi wa jama’a hidima da kare duk wani bangare na al’umma.

Gumel ya kara da cewa rundunar ‘yan sandan tana cike da bakin ciki tare da jajantawa ‘yan uwa da abokanan marigayin.

Ana ci gaba da bincike domin gano gaskiyar lamarin da kuma tantance wadanda ake zargi a Kuma damke su.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?