Majiyyaci na farko a duniya da aka dasa wa ƙodar alade ya mutu, kusan watanni biyu bayan tiyata.
A watan Maris, Babban Asibitin Massachusetts ya dasa wa Rick Slayman, wani dattijo mai shekaru 62 da ke fama da cutar ƙoda a matakin ƙarshe ƙodar aladen.
Aikin ya kasance wani muhimmin ci gaba a fannin xenotransplantation – dashen gaɓoɓin jiki ko ƙwayoyin halitta daga wani nau’in halitta zuwa wani – a matsayin mafita ga ƙarancin sassan jiki a duniya, inji asibitin a lokacin.
Asibitin ya ruwaito cewa mutuwar Slayman ba ta da alaƙa da dashen.
“Iyalanmu sun yi matuƙar baƙin ciki game da mutuwar ƙaunataccenmu Rick, amma mun ji daɗi da sanin cewa ya zaburar da mutane da yawa,” inji danginsa ranar Lahadi.
Iyalin Slayman sun yabawa tawagar likitocin da suka kula da shi.
“Babban ƙoƙarin da suka yi na jagorantar xenotransplant ya ba danginmu ƙarin makonni bakwai tare da Rick, kuma abubuwan da muka yi a lokacin za su kasance a cikin ranmu da zuƙatanmu.”
Asibitin ya ce “ya yi matuƙar bakin ciki” da mutuwar Slayman.
“Ba mu da wata alama cewa sakamakon dashen da aka yi masa ne kwanan nan.
“Slayman zai kasance har abada a matsayin ginshiƙi na fata ga marasa lafiya da yawa a duk duniya kuma muna matuƙar godiya ga amincewarsa da kuma muradinsa na ciyar da fannin xenotransplantation,” inji ta.