Back

Mutumin da ya fi kowa shekaru a duniya ya mutu

Juan Vicente Perez Mora

Wani mutum ɗan ƙasar Venezuela, Juan Vicente Perez Mora, wanda Kundin Duniya na Guinness ya tabbatar da shi a shekarar 2022 a matsayin mutum mafi shekaru a duniya, ya rasu ranar Talata yana da shekaru 114.

Shugaban Ƙasar Venezuela, Nicolas Maduro ne ya sanar da hakan ta kafar sada zumunci ta X, yana mai cewa Juan Vicente Perez Mora ya rasu yana da shekaru 114.

Guinness ta tabbatar da Perez a matsayin mutumin da ya fi kowa tsufa a duniya a raye a ranar 4 ga Fabrairu, 2022, lokacin yana da shekaru 112 da kwanaki 253.

Mahaifin 11, a shekarar 2022 yana da jikoki 41, tattaɓa kunne 18 da ‘ya’yan tattaɓa kunne 12.

An haifi manomin, wanda aka fi sani da Tio Vicente, a garin El Cobre na jihar Tachira ta Andean a ranar 27 ga Mayu, 1909, kuma shi ne na tara a cikin yara 10.

“A lokacin da yake ɗan shekara biyar, ya fara aiki tare da mahaifinsa da ‘yan uwansa a harkar noma kuma ya taimaka da girbin rake da kuma kofi,” inji sanarwar Guinness daga 2022.

Perez ya zama sheriff kuma yana da alhakin warware rikice-rikicen filaye da na iyali, yayin da yake aiki a harkar noma.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?