Back

Access Holdings, ya tabbatar da Mutuwar Herbert Wigwe

Kamfanin Access Holdings ya tabbatar da mutuwar Babban Jami’in Gudanarwa na Kamfanin Herbert Wigwe.

Wigwe ya mutu ne a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a ranar Juma’a tare da matarsa, ɗansa, da kuma tsohon Shugaban Rukunin Kamfanonin Hada-hadar Kuɗi na Najeriya (Nigerian Exchange Group Plc.), Abimbola Ogunbanjo.

Bankin, a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi mai ɗauke da sa hannun Sakataren Kamfanin, Sunday Ekwochi, ya tabbatar da afkuwar lamarin.

“Muna cike da baƙin cikin sanar da rasuwar Daraktocin Access Holdings Plc. Dr. Herbert Wigwe, CFR, Babban Jami’in Gudanarwar Rukunin Kamfanonin wanda ya Kafa Kamfanin kuma tsohon Manajan shirye-shirye na Babban Bankin Access. Plc. Dr. Herbert Wigwe wanda ya rasu tare da matarsa ​​da ɗansa a ranar Juma’a tara ga watan biyu na shekarar nan a wani hatsarin jirgi mai saukar ungulu a Amurka.”

An ba da rahoton cewa suna kan hanyar zuwa Boulder City, Nevada daga Palm Springs, California, a daren Juma’a, lokacin da jirgin mai saukar ungulu da ke jigilar su ya yi haɗari da misalin ƙarfe goma na dare, kusa da wani ƙaramin gari a cikin Desert Mojave na California, a kasar Amurka.

Mutane shida ne ke cikin jirgin mai a lokacin da ya faɗo kusa da iyakar California da Nevada. Babu wanda ya tsira daga hatsarin.

Ba a dai san ainihin abin da ya kai ga faɗuwar jirgin EC-130 ba.

Karanta cikakken bayanin a ƙasa:

ACCESS HOLDINGS PLC TA SANAR DA RASUWAR SHUGABAN RUKUNIN KAMFANONIN TA, DR. HERBERT WIGWE, CFR

Tare da takaici ne Hukumar Gudanarwar Access Holdings Plc (‘Kamfanin’) ta sanar da rasuwar Dr. Herbert Wigwe, CFR, Babban Jami’in Gudanarwar Rukunin Kamfanonin wanda ya Kafa Kamfanin kuma tsohon Manajan Darakta na Babban Bankin Access Plc. (‘Banki’). Dr. Wigwe ya rasu tare da matarsa ​​da ɗansa a ranar Juma’a 9 ga Fabrairu, 2024 a wani hatsarin jirgi mai saukar ungulu a ƙasar Amurka.

Dukkanin Iyali na Access suna jimamin rashin Herbert, Doreen da Chizi. Muna miƙa ta’aziyyarmu ga ‘yan uwa da masoyansa. Dokta Wigwe ya kasance mutum ne mai tasiri wanda ya kawo kyakkyawan sha’awarsa, kuzari, da gogewarsa ga sauyi na Bankunan Access tun lokacin da ya shiga Bankin a 2002. Da yake tsokaci game da tafiyar Dr. Wigwe, Mr. Abubakar Jimoh, Shugaban Kamfanin Access Holdings ya ce:

“Iyalin Access sun yi babban rashi da rasuwar Dr. Wigwe wanda aboki ne na ƙwarai kuma nagartaccen mutum. Yana da hazaƙa, kyawawan halaye, da kuma gogewar kasuwancin da ya kawo wa Iyalin Access wanda a kansa yana bin mu bashin godiya.

“A daidai da manufofin Kamfanin, nan ba da daɗewa ba hukumar za ta sanar da naɗin Muƙaddashin Babban Jami’in Gudanarwa na Kamfanin duk da cewa muna da ƙwarin gwiwa cewa ƙungiyar Access za ta ci gaba da ginawa a kan gadon Dokta Wigwe na ci gaba da kyakkyawan aiki.”

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?