Back

Na yi tsammanin zan riga Wigwe mutuwa, inji Sarki Sanusi

Sarki Sanusi a wajen taron

Shugaban ɗarikar Tijjaniyya kuma Sarkin Kano na 14, Alhaji Muhammadu Sanusi II,
ya zubar da hawaye har sau uku a wajen taron tunawa da shugaban rukunin kamfanonin Access Holdings kuma tsohon manajan daraktan Bankin Access, marigayi Mista Herbert Wigwe, a Legas jiya.

Hakan ta faru ne sa’ilin da yake jawabi kan mu’amalar sa ta abota da Wigwe, wanda ya mutu a wani haɗarin jirgin sama mai saukar ungulu, tare da matar sa, Doreen, ɗan sa Chizzy da kuma tsohon Manajan Darakta na hukumar musayar kuɗaɗe ta Nijeriya, Abimbola Ogunbanjo, a Amurka.

An yi taron ne domin karramawa ga Wigwe.

A duk lokacin da ya ke hawayen, sai da Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, da Aig-Imoukhuede da wani mataimaki suka riƙa ba shi haƙuri. Wani hadimin sa kuma ya riƙa kare fuskarsa da ke hawaye da babbar rigar sa daga masu kallo.

A jawabin, mai ɗaukar hankali, Sarki Sanusi ya ce saboda kyautatawar da Herbert Wigwe ya riƙa yi masa da iyalansa, wasu sun yi ɗauka cewa shi ne ma mamallakin Bankin Access, wai Aig-Imoukhuede da Herbert ɗin suna nuna kamar nasu ne kawai.

Ya ce: “A ranar Asabar ce, ban san abin da ya faru ba, na zo filin jirgi ina jiran jirgi sai Bola Adeshola ya kira ni, muna magana. Bayan ya yi magana biyu, sai ya ce, ‘Lamido ba ka ji abin da ya faru ba?’

“Kimanin shekaru biyu da suka gabata, na sanya duk abin da na tara a cikin wani asusun banki don ilimin yara na, ina da ‘ya’ya da yawa kuma fifiko na a matsayi na na uba shi ne tabbatar da cewa idan na mutu za su sami ingantaccen ilimi. Na ce wa Herbert, ‘Na ba ka ikon kula da wannan asusun don karatun ’ya’ya na domin na san cewa ko da na mutu ban bar kuɗi ba, za ka ilimantar da ‘ya’ya na.’

“Na yi tsammanin zan mutu kafin Herbert.” Da faɗin haka sai ya fashe da kuka yayin da

Ya ci gaba da cewa, “Lokacin da na samu matsala a Kano, na kira shi kusan watanni shida kafin in bar Kano, na ce masa, ‘Herbert, na san za ka yi iya ƙoƙarin ka don magance waɗannan matsalolin, amma na gamsu cewa wannan shi ne abin da zai faru’.

“Sai ya ce da ni, ‘Mai Martaba, kada ka damu, duk abin da zai faru, kada ka damu, muna nan tare da kai.’

“A ranar da na ji a rediyo an sauke ni daga gadon sarauta, da daddare kafin abin ya faru, na yi waya na ce ina so in zo Legas. An bayyana hakan ne da misalin ƙarfe tara na safe. Da tsakar rana Herbert ya aika da jirgi Kano. Na sa iyali na a cikin jirgin, babu saƙo, ba kiran waya, na sanya su a cikin jirgin. Herbert ya karɓe su, ya ajiye su a otal, kuma daga baya ya ba su masauki na watanni. Da na zo muka zauna a wurin.

“Wasu mutane sun yi imanin cewa ni ne mai Bankin Access kuma Aig da Herbert suna tsaya mani ne. Sun ba ni motoci da direbobi, sun ba ni tsaro da jirgin sama kuma ba su nemi komai ba kuma ba su yi magana a kai ba. Na zauna a Legas na tsawon shekaru huɗu, gidan da iyali na ke zaune, Herbert ne ya samar da shi.

“Lokacin da na ji labarin mutuwar sa, na ce a cikin makwanni da watanni masu zuwa mutane za su san Herbert. Sun san shi a matsayin ma’aikacin banki, a matsayin ɗan kasuwa, ba su san shi a matsayin mutum ba.

“Yana yi jama’a aiki ne, ba kansa ba. Ba za ku iya tunanin yadda mutum ɗaya zai iya zama abubuwa da yawa ga mutane da yawa ba.

“Rana ɗaya kafin abin ya faru, ina cikin wata tattaunawa a kafar sada zumunta lokacin da wani ya yi wasu kalamai game da Herbert da na ji haushi kuma na kare Herbert. Na bayyana ra’ayi na a fili cewa wannan bai dace ba kwata-kwata.

“Kwanaki kaɗan bayan mutuwar Herbert, wani aboki na ya kira ni ya aiko min da saƙo. Ya aika da saƙo zuwa ga Herbert da misalin ƙarfe 3:20 na safiyar wannan rana (ranar da haɗarin ya faru), yana gaya masa yadda na kare shi kuma ya tura masa saƙonni na gaba ɗaya.

”Herbert ya ba da amsa da ƙarfe 3:28 na safe da kalma ɗaya: ‘abin mamaki’. Ya sake aika wani saƙon da ƙarfe 3:50 wanda bai isar ba. Daga bayanan masu kula da zirga-zirgar jiragen sama, haɗarin ya faru ne da ƙarfe 3:30. Don haka mai yiwuwa, abu na ƙarshe da Herbert ya karanta shi ne saƙo na da na aika a kan sa.”

Baya ga Sarki Sanusi, wasu mutane da suka halarci taron sun haɗa da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote; shugaban kamfanin Coronation, Aigboje Aig-Imoukhuede; shugaban kamfanin Berkeley Plc, Henry Imasekha, da sauran su.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?