Shugaban Rundunar Sojojin Sama (CAS), Air Marshal Hasan Abubakar, ya jaddada aniyar Rundunar Sojojin Saman Nijeriya (NAF), na tabbatar da jin daɗin iyalan jaruman da suka rasu.
Abubakar ya ba da wannan tabbacin ne a lokacin da Ƙungiyar Matan Hafsan Sojin Sama ta Nijeriya (NAFOWA) ta kai agajin jin ƙai da kuma taimakon gaggawa ga zawarawan jaruman NAF da suka rasu a ranar Asabar a Abuja.
Ya ce ya zama wajibi hukumar ta tabbatar da cewa gudummawa da sadaukarwar da jama’an suka bayar ba a banza ba ne.
CAS ɗin ya ce NAF ta kafa Tsarin Inshorar Hatsari, a matsayin wani ɓangare na matakan tallafawa iyalan jaruman da suka mutu da kuma mayaƙan da suka raunata, baya ga Tsarin Rayuwa na Ma’aikatar Tsaro ga dukkan jami’ai.
A cewarsa, tsarin yana ba wa dukkan jami’an inshorar haɗura, raunuka da mace-mace a duk lokacin da irin wannan bala’i ya faru, ta yadda za su samu ƙwarin gwiwa wajen gudanar da ayyukansu da sanin cewa ana kula da lafiya da walwalar su yadda ya kamata.
“Bugu da ƙari, ina so in tunatar da masu sauraro cewa yaran duk jami’an da suka mutu a hidimar aiki suna da damar tallafin karatu na NAF har zuwa matakin manyan makarantu.
“Saboda haka ana kira ga zawarawa da su yi amfani da wannan tsarin domin tarbiyyar ‘ya’yansu.
“Ku tabbata cewa NAF za ta ci gaba da tunawa da abokan aikinmu da suka rasu tare da kula da iyalansu gwargwadon iko.
“Kamar yadda NAFOA ke nuna mana a yau, ni ma ina so in ɗan ɗauki lokaci don yabawa matanmu da ‘ya’yanmu da suke tsaye tare da mu a kowane hali.
“Ina yaba wa juriyarku da addu’a kada ƙoƙarinsu ya kasance a banza,” inji shi.
CAS ɗin ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu bisa goyon bayan da yake baiwa jami’an wanda hakan ya ƙara inganta ayyukan Rundunar.
Ya ba da tabbacin cewa NAF za ta ci gaba da yin aiki tuƙuru tare da haɗin gwiwa da takwarorinta da sauran hukumomin tsaro don magance matsalolin tsaro a ƙasar.
“Ku ba ni dama in sanar da duk ‘yan ƙasa nagari na ƙasarmu mai girma cewa za su iya tabbatar da cewa NAF ta duƙufa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a dukkan sassan ƙasar.”
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa ayyukan jin ƙai na NAFOWA sun haɗa da wayar da kan jama’a ga iyalan NAF da matan jami’an da suka rasa rayukansu.
Ƙungiyar ta kuma raba kayan abinci da suka haɗa da shinkafa, semovita, taliya, manja da man gyaɗa, wake da kuɗi ga zawarawa 100.
Shugabar Ƙungiyar ta NAFOWA, Misis Rakiya Abubakar, ta ce ƙungiyar za ta tallafawa dukkan zawarawan jaruman NAF da suka rasu a wajen Abuja ta rassanta.
Ta kuma nemi tallafin masu hannu da shuni da ƙungiyoyi don sanya murmushi a fuskokin iyalan jami’an da suka rasa rayukan su.