Back

Najeriya na da mashaya miyagun kwayoyi miliyan sha hudu, hakan ke ta’azzara fashi, garkuwa da mutane – NDLEA

Hakan ya fito ne daga bakin kwamandan shiyyar ‘F’ na hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ACGN Sule Momodu, inda ya nuna cewa karuwar masu shan miyagun kwayoyi a kasar nan shi ne tushen sahihancin ‘yan fashi da sauran laifuka.

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta yi ikirarin cewa adadin masu ta’ammali da miyagun kwayoyi a kasar ya kai kimanin miliyan goma Sha hudu da dubu dari Uku.

Hakan ya fito ne daga bakin kwamandan shiyyar ‘F’ na hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ACGN Sule Momodu, inda ya nuna cewa karuwar masu shan miyagun kwayoyi a kasar nan shi ne tushen sahihancin ‘yan fashi da sauran laifuka.

Momodu ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da masana harhada magunguna da jami’an soji da sauran jami’an tsaro a wata tattaunawa da suka yi na dakatar da yaduwar miyagun kwayoyi a jihar Kaduna.

Ya bayyana cewa, magance matsalar rashin tsaro shi ne ke kawo cikas ga nasarorin da Najeriya ke samu na ci gaba mai dorewa da kuma sauran manufofin ci gaba na gwamnati, yayin da amfani da muggan kwayoyi ya kasance babban sanadin yawaitar sace-sacen mutane da garkuwa da mutane a kasar.

Shugaban hukumar ta NDLEA ya ce, “Akwai masu shan miyagun kwayoyi miliyan goma sha hudu da dubu dari Uku a Najeriya. Yawan yaduwar tu’ammali da muggan kwayoyin a jihar Kaduna kadai ya kai kashi goma cikin dari, inda ya zamanto na hudu a jihohin Arewa maso Yamma na kasar nan. Yankin Arewa maso Yamma kadai yana da kusan miliyan uku masu amfani da kwayoyin.”

Ya kara da cewa a lokacin yana Kwamandan NDLEA a Katsina, gwamnan jihar ya shawarce shi da cewa da zarar ‘yan bindiga sun yi amfani da tramadol, babu abin da zai hana su aiwatar da munanan ayyukan su.

Aliyu Jibrin, wani kwararre a fannin hada magunguna da ya yi magana a madadin takwarorin shi, ya bayyana cewa, masana harhada magunguna a matsayin su na kwararru, suna sane da  ka’idojin kawar da muggan kwayoyi kuma ba za su yi wani abu da zai kawo cikas ga tsaron Najeriya ba.

Ya ce masu harhada magunguna a Najeriya ba su da iyaka, inda ya ce a duk fadin Kaduna ba su kai mutum dari hudu ba; duk da haka akwai dubban shagunan sayar da magunguna a jihar.

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?