Back

Nasarawa za ta biya kuɗaɗen rubuta jarrabawar NECO ga ɗaliban shekarar ƙarshe

Gwamnatin jihar Nasarawa ta ce za ta biya kuɗin rajistar Hukumar Shirya Jarrabawa ta Ƙasa (NECO) na shekarar 2024 ga duk ɗaliban da suka kammala karatu a makarantun gwamnati a jihar.

Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ƙaddamar da sabbin sakatarorin dindindin guda huɗu da aka naɗa, da kuma shugaban zartaswa da mambobin Hukumar Kare Haƙƙin Naƙasassu ta jihar Nasarawa, a gidan gwamnati da ke Lafia jiya.

Gwamnan ya kuma ce gwamnatin sa za ta fara rabon kayan abinci a matsayin tallafi ga ɗaukacin ɗaliban ƴan asalin jihar da ke makarantun gaba da sakandare.

Ya ce gwamnatinsa ta yanke shawarar biyan kuɗaɗen rajistar ɗaliban shekarar ƙarshe da zasu rubuta NECO, tare da raba kayayyakin tallafi ga ɗaliban manyan makarantu, a wani ɓangare na ƙoƙarin rage wahalhalun da ake fuskanta a faɗin ƙasar nan.

Ya nanata cewa shugaba Bola Tinubu yana da cikakkiyar masaniya kan irin wahalhalun da ƴan Nijeriya ke ciki, kuma shugaban ya na aiki tuƙuru ta hanyar gwamnoni da sauran hukumomi, domin daƙile illolin.

Wakilinmu
Wakilinmu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?