Hukumar Kwastam ta Nijeriya ta sake buɗe iyakar ƙasa da ƙasa a garin Kamba da ke ƙaramar hukumar Dandi a jihar Kebbi domin bunƙasa harkokin kasuwanci tsakanin Nijeriya da Jamhuriyar Nijar da Benin.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar reshen jihar Kebbi, SC Mohammed Tajuddeen-Salisu, da ya bayyanawa manema labarai a Birnin Kebbi ranar Lahadi.
Ya ce, “Sabon Kwanturolan Hukumar Kwastam (CAC), reshen Jihar Kebbi, Mista Iheanacho Ernest-Ojike, a ranar Juma’a, ya sake buɗe iyakar ƙasa da ƙasa kamar yadda Shugaban Hukumar Kwastam, Mista Bashir Adewale-Adeniyi ya bayar da umarni.
Sanarwar ta ruwaito Ernest-Ojike na cewa an sake buɗe iyakar da nufin share fagen kasuwanci na halal da zai yi tasiri ga gina ƙasa.
“Wannan ba izini ba ne na shigo da haramtattun abubuwa da za su yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa da kuma kawo cikas ga tsaron ƙasa,” inji shi.
“Jami’an ‘yan sanda a shirye suke su sauƙaƙa kasuwancin halal kuma su yi aiki bisa tsarin doka don sauƙaƙa kasuwanci a iyakar Kamba.”
Wannan shi ne “muddun masu ruwa da tsaki sun shigo da abin da dokokin kwastam suka ba da izini, suka bayyana yadda ya kamata tare da biyan kuɗaɗen da suka dace ga asusun Gwamnatin Tarayya”.
Kazalika kakakin ya ruwaito CAC yana cewa har yanzu an hana fitar da kayan abinci zuwa ƙasashen waje, duba da yadda al’ummar ƙasar ke fama da ƙarancin abinci a halin yanzu.
Hakimin Kamba, Alhaji Mamuda Fana, ya yabawa ƙoƙarin Gwamnatin Tarayya, yana mai cewa wannan wani sabon fata ne ga al’ummarsa masu sha’awar sana’o’in da ke kan iyaka, da ma ƙananan ‘yan kasuwa mazauna yankin.
“Na yi wa Gwamnatin Tarayya da NCS alƙawarin cewa za a gargaɗi jama’ata game da haramtacciyar kasuwanci da kuma fa’idar sake buɗe iyakar ƙasar nan,” inji shi.