Back

NDLEA ta kama ma’aikatan tashar jirgin ruwa da hodar iblis, tabar wiwi sama da kilogiram miliyan ɗaya da arba’in

Jami’an Hukumar Yaƙi da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) a ranar Lahadi sun bayyana cewa, sun bankaɗo wasu ‘yan ƙungiyar masu aikata laifuka waɗanda suke yunkurin shigo da kwantena guda biyu da ke ɗauke da miyagun ƙwayoyi kwanan nan.

NDLEA, a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi mai ɗauke da sa hannun Daraktan Yaɗa Labarai da Bayar da Shawarwari, Femi Babafemi, ta kuma bayyana cewa an yi safarar makamai da alburusai iri-iri daga Durban na ƙasar Afirka ta Kudu zuwa tashar ruwan Tincan da ke Legas.

Hukumar ta ce daga cikin waɗanda aka kama a matsayin ‘yan ƙungiyar akwai masu tantance kwantena guda biyu, Falowo Samuel Kayode; mai lodin kaya, Anjorin Idowu; da Uzairu Ahmed Iguda, wanda ke kula da ɗakin saukan fasinjoji a tashar jiragen ruwan.

Sai dai, ya ce har yanzu ba a kama wani mai lodin kaya a tashar, Mohammed Muktar Sule (wanda aka fi sani da organiser) ba wanda kuma ke da alaƙa da ƙungiyar.

“Bisa ga sahihan bayanan sirri, hukumar ta buƙaci a tantance kwantenan guda biyu masu lamba MSCU 4581770 da TRHU 7968071 daga Afirka ta Kudu. Sakamakon haka, an gudanar da aikin tare da sauran masu ruwa da tsaki a ranakun sha takwas da sha tara ga watan daya na wannan shekarar, inda aka ƙwato kilogiram hamsin da shida da ɗigo talatin da tara na hodar iblis da kilogiram ɗari bakwai da tamanin da biyar na wani Colorado, wani nau’in tabar wiwi mai ƙarfi da sauran haramtattun kayayyaki a cikin kwantenan.

“Bayan umarnin da Shugaba kuma Babban Jami’in Hukumar NDLEA, Brig. Janar Mohamed Buba Marwa (Mai Ritaya) ga wata tawagar ƙwararru na hukumar domin bankaɗo masu hannu da shuni wajen shigo da miyagun ƙwayoyi, binciken da ake yi ya kai ga gano ƙarin jakunkuna na tabar wiwi mai nauyin kilogiram ɗari da tamanin da biyu da ɗigo bakwai, bindiga, da harsasai da aka cire daga cikin kwantena mai lambar MSCU 4581770 kuma an ɓoye su a cikin wani kwantena da babu komai a ciki kafin tantancewar kashi ɗari a tashar.

“Saboda haka, an kama wasu mutane biyu: Uzairu Ahmed Iguda wanda ke kula da ajiye kwantena a tashar, da Anjorin Idowu wanda yake lodin kaya a tashar. Wani wanda ake zargi, Mohammed Muktar Sule (wanda aka fi sani da organiser) wanda a yanzu ba a kama ba, shi ma mai lodin kaya ne a tashar. Bincike ya nuna cewa mutane ukun da ake zargin sun haɗa baki ne da mai tantance kwantenan guda biyu, Falowo Samuel Kayode, inda suka kwashe kilogiram ɗari da tamanin da biyu da ɗigo bakwai na tabar wiwi, bindiga da harsasai daga cikin kwantenan zuwa wani kwantena da babu komai a ciki a tashar.

“Ƙwacen da aka yi daga kwantenan biyu ya kai jimilla kilogiram hamsin da shida da ɗigo talatin da tara na hodar iblis da kilogiram ɗari tara da tamanin da bakwai da ɗigo tara na tabar wiwi waɗanda nauyin su duka ya kai kilogiram miliyan ɗaya da arba’in da huɗu da ɗigo ashirin da tara. Bincike ya kuma nuna wasu shugabanni uku na ƙungiyoyin ana kyautata zaton suna zama ne a Afirka ta Kudu kuma suna da alaƙa da shigo da kwantenan. Sun haɗa da: Odeyemi Taiwo Emmanuel; Akinyemi Olayinka da Adebayo Adewole Emmanuel waɗanda yanzu haka ke cikin jerin waɗanda hukumar ke nema ruwa a jallo.”

Wakilin Mu
Wakilin Mu
https://www.btvhausa.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

× Yaya zan iya taimaka ma ku?